Juan Antonio Samaranch Jr.: Gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta zarce tunanin IOC

Daga CRI HAUSA

Bisa la’akari da yaɗuwar annobar COVID-19, ayyukan shirya gasar Olympics ta lokacin huturu ta Beijing, sun kasance masu matuƙar wahala, sai dai sun samu kyakkyawan yabo.

Shugaban kwamitin taimakawa shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta shekarar 2022 na kwamitin wasannin Olympic na duniya IOC, wato Juan Antonio Samaranch Jr. ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, duk da muhawarar da ake tafkawa kan ƙasashe masu karɓar baƙuncin gasanni da kwamitocin shirya gasannin, kwamitin IOC bai taɓa shakkun ƙarfin ƙasar Sin na karɓar baƙuncin gasar ba, haka kuma ayyukan shirya gasar da aka yi, ba kawai cimma mizanin kwamitin IOC kaɗai suka yi ba, har ma da zarce tunaninsu.

A ƙoƙarin tabbatar da gudanar da gasar yadda ya kamata, ana gudanar da gasar tare da sa ido da taƙaita zirga-zirgar ‘yan wasa da jami’ai. A cewar Juan Antonio Samaranch Jr., hukumomin kula da lafiyar al’umma na ƙasar Sin sun yi aiki tuƙuru, inda wannan mataki da suka ɗauka, ya taka muhimmiyar rawa wajen gudanar wasannin ba tare da wata tangarɗa ba kawo yanzu.

Ya ƙara da cewa, gasar ta lokacin hunturu ta Beijing, za ta yi kyakkyawan tasirin kan zuriyoyi masu zuwa, kamar yadda gasar ta lokacin zafi ta shekarar 2008 ta yi.

Bugu da ƙari, ya ce ƙasar Sin na da wuraren wasanni na gani na faɗa, waɗanda za su cimma buƙatun al’ummar ƙasar cikin shekaru da dama masu zuwa, yana mai cewa, ba kwanaki 16 kaɗai, sai an kai fiye da shekaru 60. Ya ci gaba da cewa, ababen more rayuwa kamar jiragen ƙasa masu sauri da manyan tituna, na da matuƙar muhimmanci ga al’umma, za su ƙara ingancin rayuwar jama’a.