Sojojin Nijeriya 68 za su gurfana gaban shari’a saboda take doka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana shirin hukunta dakarunta guda 68 saboda samun su da aikata laifuffuka daban-daban, lokacin da runduna ta 8 dake Sakkwato ke gudanar da sintirin kakkaɓe ‘yan ta’adda a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Katsina.

Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Uwem Bassey dake kuma jagorancin rundunar da ake kira ’Hadarin Daji’ ya bayyana haka lokacin da yake qaddamar da kotun da za ta gudanar da shari’ar.

Janar Bassey wanda ya yi suna wajen kutsa kai sansanonin ‘yan ta’adda yana kai musu hari, ya buƙaci alƙalan da za su yi shari’ar da su tabbatar da adalci dangane da zargin da ake yi wa sojojin.

Kwamandan ya ce lura da cewar waɗanda za su gurfana a gaban kotun sojoji ne kamar su, saboda haka suna buƙatar girmamawa da kuma adalci.

Janar Bassey ya yi alƙawarin cewar kotun za ta yi amfani da kundin tsarin mulkin shekarar 1999 wajen gudanar da shari’un dake gabanta.