Sufeton ƴan sanda ya umarci a ɗauki mataki akan waɗanda suka kai hari ofishin rundunar a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya umarci a ɗauki mataki akan waɗanda suka kai hair a ofishin rundunar dake Nganzai a Jihar Borno.

A ranar Alhamis ne harin mayaƙan Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar ƴan sanda biyu a yayin wani ba-takashi tsakanin ɓangarorin biyu inda aka samu ɗauki daga jami’an haɗaka na CJTF.

A lokacin da ya ke tsokaci game da lamarin, Sufeton ƴan sandan ta ofishin jami’in yaɗa labaran rundunar, Muyiwa Adejobi ya bayyana sunayen jami’an da suka rasa rayukan nasu a matsayin Sufeto Bartholomew Kalawa da kuma Koforal Mustapha Huzaifat.

Kakakin rundunar ya ce Sufeton, bayan yin alla-wadai da harin, ya kuma umarci gudanar da bincike mai zurfi tare da hukunta waɗanda aka samu da hannu acikin lamarin.

Sufeton ya kuma aika da saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukan nasu, ya na mai cewa za a riƙa tunawa da sadaukarwarsu ga al’umma.

Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a biya iyalan jami’an kuɗaɗen ƙa’idar da aka amince da su hukumance.

By ukarofi