Firayim Ministan Canada Justin Trudeau ya sanar da murabus ɗinsa a ranar Litinin ɗin da ta gabata, yana mai cewa, zai bar mulki da zarar jam’iyyar Liberal mai mulki ta zaɓi sabon shugaba bayan shafe watanni ana fama da zaɓukan cikin gida.
“Ina da niyyar yin murabus a matsayin shugaban jam’iyyar, a matsayina na Firayim Minista, bayan da jam’iyyar ta zaɓi shugabanta na gaba ta hanyar ingantaccen tsarin zaɓe a faɗin kasar,” Trudeau ya fadawa manema labarai a Ottawa.
“A daren jiya, na nemi shugaban jam’iyyar Liberal Party da ya fara wannan aiki,” Trudeau, wanda ke kan karagar mulki tun shekarar 2015, ya shaida wa manema labarai a birnin Ottawa, biyo bayan dambarwar siyasar da ta daɗe, wadda ta yi sanadiyar manyan ‘yan Liberal suka buƙaci ya yi murabus.
Ba a dai bayyana tsawon lokacin da Trudeau zai ci gaba da zama a ofis a matsayin firayim ministan riƙo ba.