Wani alƙali a birnin New York, mai shari’a Juan Merchan, ya ba da umarnin a yanke wa Donald Trump hukunci a ranar 10 ga watan Janairu, a shari’ar da ake masa na badaƙalar kuɗi a New York, ƙasa da makonni biyu kafin a rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.
Mai shari’a na New York Juan Merchan ya yi ishara da cewa, ba zai yanke wa Trump hukuncin zaman gidan yari, aikatau, ko kuma tara ba, a maimakon haka ya ba shi “sallama ba tare da wani sharaɗi ba,” ya kuma rubuta a cikin umarninsa cewa, zaɓaɓɓen shugaban na iya bayyana da kansa ko kuma aike don sauraron ƙarar.
Trump ya yi yunƙurin yin amfani da nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa wurin ganin an yi watsi da ƙarar da ake masa.
Zaɓaɓɓen shugaban aasar ya wallafa a shafukan sada zumunta inda ya yi watsi da umarnin alƙalin a matsayin “Hare-haren haramtacciyar siyasa,” tare da kiran shari’ar da cewa “ba komai ba ce illa cin hanci da rashawa.”
An yanke wa Trump hukunci a watan Mayu da laifuka 34 da suka shafi bayanan bugi kan kasuwanci da suka shafi dala 130,000 (£ 105,000) da kuma biyan Toshiba baki ga wata babbar jarumar finafinan batsa, Stormy Daniels.
Zarge-zargen da ake zargin sun shafi yunƙurin ɓoye kuɗaɗen da aka biya wa tsohon lauyansa, Michael Cohen, wanda a kwanakin ƙarshe na yaƙin neman zaɓen 2016 ya biya wata babbar jarumar finafinan batsa toshiyar baki, don ta yi shiru game da mu’amalar da ta shiga tsakanin ta daTrump.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar dai ya musanta aikata duk wani laifin da ya aikata, ya kuma musanta aikata laifin, yana mai cewa shari’ar wani yunƙuri ne na cutar da yaƙin neman zaɓensa na 2024.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth a Jiya, Trump ya ce, hukuncin da alƙali ya yanke “ya saɓa wa kundin tsarin mulkinmu, kuma idan aka ba mu damar tsayawa, zai zama ƙarshen shugabancin ƙasar kamar yadda muka sani.”
Shi kuwa kakakin Trump Steɓen Cheung, ya kira umarnin wani ɓangare na “bi ta da ƙulli.”
“Dole ne a bar shugaba Trump ya ci gaba da aiwatar da tsarin miƙa mulki na shugaban ƙasa da kuma aiwatar da muhimman ayyuka na shugabancin ƙasa, ba tare da cikas daga irin waɗannan ko sauran masu bi ta da ƙulli ba,” inji Cheung.
Ya ƙara da cewa, “Bai kamata a yanke hukunci ba, kuma shugaba Trump zai ci gaba da yaƙi da waɗannan labaran ƙarya har sai sun mutu.”
A cikin sabon kudirin da ya gabatar na kin amincewa da shari’ar, Trump ya yi zargin cewa shari’ar za ta rataya a kansa a lokacin da yake shugabancin ƙasar tare da kawo masa cikas a harkokin mulki.
Mai shari’a Merchan ya ce, an ba shi shawarar wasu matakai da zai iya amfani da su waɗanda za su iya rage damuwar Trump game da karkatar da hankalinsa kan shari’ar yayin da yake shugabantar ƙasa, inda ya ne ma wa kansa “babbar mafita” ta kifar da alƙalan kotun.
Zaɓuɓɓukan nasa sun haɗa da jinkirta yanke hukuncin har sai Trump, mai shekaru 78, ya bar fadar White House a 2029, ko kuma ba da tabbacin hukuncin da ba zai shafi zaman gidan yari ba.
Tun da farko Trump ya yi iya mai yiwa don ganin ya kawar da shari’ar, saidai bai yi nasara ba, ya bayar da hujjar cewa, shari’ar da ake yi masa ta ci karo da hukuncin da kotun koli ta yanke kan kariyar shugaban ƙasa.
A watan Yuli, babbar kotun ƙasar ta yanke hukuncin cewa, shugabannin ƙasar suna da babbar kariya daga tuhume-tuhume kan “ayyukan hukuma” da suka ɗauka yayin da suke kan karagar mulki.
Sai dai a watan da ya gabata mai shari’a Merchan ya yanke hukunci kan badaƙalar kuɗaɗen da ake zargin Trump da aikatawa.
A halin yanzu dai Trump na shirin zama mutum na farko da aka samu da laifi da zai yi aiki a fadar White House.
Saidai yana da damar yunƙurin ɗaukaka ƙara a kan hukuncin bayan yanke hukuncin.
Duk da yake laifin coge kan bayanan kasuwanci na da girma sosai, wanda zai iya kai hukuncin ɗauri har zuwa shekaru huɗu a gidan yari a Amurka.
Tun kafin nasarar zaɓensa, masana harkokin shari’a sun yi tunanin cewa da wuya Trump ya fuskanci zaman gidan yari idan aka yi la’akari da shekarunsa da kuma tarihinsa na shari’a.
An kuma tuhumi Trump a cikin wasu laifuka uku na jiha da na tarayya: ɗaya da suka shafi wasu takardu na sirri da kuma biyun da suka shafi ƙoƙarin tada ƙayar baya a shan kayen da ya yi a zaɓen 2020.
Tun a ranar 26 ga watan Nuwamba ne aka shirya yanke wa zaɓaɓɓen shugaban hukunci, amma mai shari’a Merchan ya ja da baya bayan Trump ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.