Tare da CHIROMA AMINU ASID
Mafi yawan mutane suna ɗauke da cutar hanta (Viral Hepatitis). Ciwon kumburin hanta cuta ce da ke ɓoye kanta a cikin jikin mutum, wacce za ka iya share sama da shekaru 30 ɗauke da wannan cutar, amma kai ba ka sani ba har sai lokacin da hantar ya lalace.
Wasu daga cikin muhimman ayyukan da hanta ke yi sun haɗa da:
1. Hanta tana tace jini tare da ware guba, ƙwayoyi, barasa da duk wani abu mai cutarwa, wanda jiki ba ya buƙata.
2. Hanta ke samar da sinadaran ɗaukewar jini (clotting factors). Sinadaran ne ke ɗaukewar jini, idan aka samu rauni, jinin al’ada, jinin naƙuda a lokacin haihuwa da sauransu.
3. Hanta ke samar da sinadarin narke kitse a cikin hanji.
4. Hanta ke samar da kuzarin jiki ta hanyar sarrafa sinadarin ‘carbohydrates’ tare da daidaita sikarin jini (blood glucose level).
Daga lokacin da hanta ta samu matsala, to babu waɗannan muhimman ayyukan.
ƙwayar cutar ‘Viral Hepatitis A, B, C, D da E, waɗanda a cikinsu (B da C) sun fi hatsari ga lafiyar mutum, suna lalata hantar mutum ta hanyar kumburar da ita, wato ‘liver inflammation’ da Turanci.
Hanyoyin da ake ɗaukar wannan ƙwayar cutar sun haɗa da:
1. Haɗuwar jini kai tsaye: Musayar jini ta hanyar amfani da allura, reza, wuƙa, wurin aski ko kuma a wurin cire ƙumba da sauransu.
2. Jima’i: Saduwa ta hanyar jima’i, sumbata ko rungume-rungume.
3. Uwa zuwa jariri: Jariri zai iya ɗaukar wannan cutar a wurin mahaifiyarsa, musamman a lokacin haihuwa.
4. Kayan amfanin gida: Amfani da kayan amfanin gida na wani, misali abin goge baki, sabulu, ɗan kunne, tufafi da sauransu.
Alamomin kamuwa da wannan ƙwayar cutar:
Kasala, mura, rashin cin abinci, ramar jiki, ciwon ciki, fitsari mai duhu, yin bahaya mai haske ko kuma ‘jaundice’, wato canjawar launin ƙwayoyin ido.
Wannan cuta tana ta kashe mutane da yawan gaske, amma kuma abun mamaki shine mutane ba su mayar da hankali wurin zuwa asibiti, domin gwaji tare da ɗaukar matakin gaggawa ba.
