Ta banka wa kanta wuta saboda tsananin kishi a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Wata mata ‘yar kimanin shekara 25 da haihuwa, ta banka wa kanta wuta saboda tsananin kishi a ƙauyen Ƙwayamawa da ke cikin ƙaramar hukumar Dutse a jihar Jigawa.

Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna cewa, sai da matar ta bulbule kanta da man fetur kana daga bisani ta cinna wa kanta wuta.

An ce bayan da ta ga uwar-bari sakamakon raɗaɗin wutar ta ke cin ta, sai ta ruga waje tana ihu tana neman taimako, inda a nan waɗanda ke kusa suka taimaka wajen kashe wutar.

Duk da dai an yi nasarar kashe wutar, amma matar ta ƙone sosai, domin kuwa kusan rabin jikinta a ƙone yake.

A halin da ake ciki, matar tana kwance a asibitin Rasheed inda likitoci ke kulawa da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *