Rundunar ’yan sanda a ƙasar Philippines sun yi kam da wani wata Nijeriya mai suna Ifeanyi Okoro tare da wasu mata uku da wani jariri da mahaifiyarsa ta sayar da shi domin biyan bashin caca.
A cewar wani rahoto da jaridar The Filipino Times ta wallafa, an zargi mahaifiyar jaririn da sayar da jaririnta mai watanni tara domin ta biya bashin da ta ciwo a lokacin cacar ‘e-sabong’ ta yanar gizo.
Rahotanni sun bayyana cewa, ’yar Nijeriyar tare da wasu mata uku ’yan ƙasar Philippines, Imelda Malibiran, Kristine Joyce Esdrelon da Rosemarie Gutierrez, sun sayi jaririn ne daga gare ta a kan Feso 45,000 (kimanin naira 500,000 kenan).
Sai dai kuma, bayan da ta sauya ra’ayi, mahaifiyar jaririn ’yar shekara 22 ta nemi taimakon hukumar NBI domin a dawo da yaron.
Hukumar bincike ta ƙasa (NBI) ce ta shigar da ƙara bayan ceto jaririn a ranar Talata 22 ga watan Maris a garin Calamba, Laguna.
Hukumar NBI ta kama Okoro da Malibiran yayin aikin ceto.
An tuhumi waɗanda aka amsa da laifin yin garkuwa da su, cin zarafin yara, cin zarafi da wariya don wasu dalilai; da fatauci.
Hukumar NBI na Hukumar yaƙi da fataucin mutane (NBIAHTRAD) ce ta bi sawun su bayan jami’an sun kwato jaririn daga hannun Ifeanyi Okoro.
