Rayuwarsu ta yi kama da rayuwar mutanen farko, waɗanda sukan yi yawo tsirara. Wasu daga cikinsu sukan ɗaura ganyayyaki a madadin tufafi.
Wannan ƙabila ba wata ƙabila ba ce illa ƙabilar ‘Gerin Jina’ da ke tsakiyar duwatsu cikin ƙaramar hukumar ‘Gashaka’ ta jihar Taraba da ke Arewa maso-gabashin Nijeriya. Rayuwar ƙabilar Gerin Jina tana da abin mamaki fiye ma da ta mutanen ‘Koma’ waɗanda ‘yan bautar ƙasa su ka gano a shekarar 1980, wanda a lokacin ake hasashen cewar al’ummar ‘Koma’ ita ce mafi koma baya a jihar Gongola.
Zamantakewa:
Waɗannan mutane da aka fi sanin su da al’ummar ‘Jibu’ ’yan asalin masarautar ‘Kwarafa’ waɗanda suka rayu da wasu karnuka waɗanda ke da rabe-raben al’adu har kashi tara da ke rarrabe akan duwatsun ‘Gashaka’ tarihi ya nuna cewa al’ummar sun yi ƙaura zuwa kan duwatsun ne sakamakon isowar jihadin ‘Shehu ɗan fodiyo’ da ya iso yankinsu, yankin da waɗannan mutane ke rayuwa wato saman dutse a ƙunshe yake da ‘koguna’, manya-manyan ƙwarurruka haɗi da manya-manyan duwatsu.
Kamar dai sauran mutane, su ma ƙabilar Jibu su na da nasu nau’ikan al’adu waɗanda suke koyi da su. Akwai lokaci na musamman da ake tara yara sa’anni, ma’ana yara waɗanda aka haifo su kusan lokaci daya domin yi masu kaciya, a wannan lokaci za a shirya ‘yar ƙwarya-ƙwaryan biki musamman domin wannan lokaci, akan yi amfani da wani abu mai kaifi a wajen yi musu kaciyar, misali abu mai kaifi kamar ‘aska’. A irin wannan yanayi ne ake samun dama domin Auna Jarumta, karfin zuciya ko kuma tantance girman juriyar waɗanda aka aiwatar da kaciyar a kansu, bayan an kammala kaciyar sai a ɗora yaran da aka yi wa kaciyar a kan gadaje irin waɗanda da aka yi su da karare daga bisani kuma a rufe su da ganyayayyaki waɗanda ake tarawa a kona su bayan kaciya ta warke.
Auratayya:
A al’adance namiji ba zai sami auren mace ba har sai ya kasance mai yi wa iyalan wannan mace hidima da bauta har na tsawon shekara biyar, sannan kuma wani abin mai cin rai shi ne, kafin a kai ga maganar aure da zama sai an gwada matar domin tantace wacce za ta iya ɗaukar ciki ko kuma akasin hakan. Akan yi wannan gwaji ta hanyar cinna wa wani gungumen itace sannan kuma busashshe wuta har na tsawon wata uku, a waɗannan watanni uku su ne damar mace na ɗaukar ciki , wanda idan kuwa har aka sami akasin haka to lallai wannan aure fa ba za a yi shi ba, dalili kuwa shi ne wannan rashin ɗaukar ciki ya nuna cewar ababen bautarsu ba su yi na’am da wannan aure ba.
Mata masu ciki su ke hoɓɓasa wajen aikin gona kama daga lokacin ɗaukar ciki har lokacin da mace za ta haihu. Mutanen garin Jina sun kasance a ƙarƙashin mulkin ‘Wazirin Garin Jina’ wato ‘Tann Shidin Zunbi’.
Addini:
ƙabilar Jiba sun kasance su ba Musulmai ba, ba kuma Kiristoci ba ne a maimakon hakan ma su sun yi imani ne da nasu ababen bauta na daban.
Abin da suka yi imani da shi, shi ne, idan har ɗaya daga cikinsu ya saɓa wata doka da aka gindaya musu na garinsu, to tabbas ya zama lalle a yanka wata dabba a wannan lokaci domin zubar da jini, al’ummar sun yi imani da cewar wannan jini da aka zubar shi ne zai zama sanadiyar sassauci ko kuma sanyaya zuciyar ababen bautarsu daga fushin na laifin da aka aikata musu.
