Taron APC: Neman jirgin fito

Daga DR. KABIRU ABUBAKAR MAGAMA

Idan akwai wani abu da na tsana a siyasa, musamman ta Nijeriya, shine biyayya, ƙwarewa da kuma sakayyar ƙoƙarin da ka yi da ke tashi a tutar babu a wajen wasu ‘yan siyasa, har ga waɗanda suke ganin kansu sun fi kowa cancanta da nagarta.

Wannan misalin shi zai nuna yadda wasu ke hamayya da takarar Sanata Abdullahi (Turakin Keffi) na neman Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa. 

Ni ba masoyin Sanata Abdullahi Adamu ba ne, amma ku faɗi duk abinda za ku faɗa akan sa, ya yi abin a zo a gani a Jihar Nasarawa lokacin da yake gwamnan jihar, kuma tabbas shi mutum ne mai biyayya ga Shugaba Buhari da kuma Jam’iyyar APC. Na sani, saboda tun ba yanzu ba Ina matuƙar bibiyar siyasarsa, kuma na zauna da ‘yan siyasa kala-kala daga jam’iyyu da dama a jihar Nasarawa da ma ƙasa bakiɗaya.

Shi mutum ne da ya samu ɗumbin nasara a cikin siyasar sa, yake kuma taka rawa tun a jamhuriya ta biyu har zuwa yau ɗin nan. Mutum ne mai ƙwarewa akan ayyukan sa, jajurtacce, mai kishin jama’a, kana ingantaccen ɗan siyasar da ke gina al’umma.

Saboda haka, ba wani abin mamaki ba ne yadda miliyoyin ‘ya’yan jam’iyyar APC suke kallon Abdullahi Adamu, Sanata mai ci a yanzu, da ke wakiltar Nasarawa ta Arewa, waɗanda suke ganin shi ne mafi dacewa kuma wanda ya ƙware a siyasa da zai iya jan ragamar jam’iyyar APC, musamman a irin wannan yanayi da jam’iyyar ta shiga tangal-tangal.

Yanzu haka APC na buƙatar ceto jam’iyyar daga dulmiyewa, jam’iyyar na buƙatar daidaito ta kowane ɓangare, ƙwarancewa, samun mai gaskiya da riƙon amana wanda zai sasasaita ta ta koma daidai.

Jam’iyyar na buƙatar jajurtaccen shugaban da zai haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar, tare kuma da samun daidaito a jam’iyyar; wanda babu wani wanda zai iya samar da hakan da ya wuce Sanata Abdullahi Adamu.

A kodayaushe ana samun mutane masu bambancin ra’ayi da manufa a siyasa ko da kuwa a jam’iyya guda suke, saboda haka rikicin cikin gida na jam’iyya ba wani sabon abu ba ne, haka kuma canja sheƙa daga waccan jam’iyya zuwa waccan. A zantuttukan su suna cewa wai masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suna ƙalubalantar takarar Sanata Abdullahi Adamu, wanda wannan ɗan ƙaramin abu ne a siyasance. 

Abin mamaki yadda Sanata Abdullahi Adamu da kan sa ya shanye duk wata barazana, suka da kace-nacen da masu hamayya da shi daga jam’iyyar suke yi masa. Bai samu sukunin yin yaqin  neman zaɓe ba, kawai abinda ya maida hankali wajen haɗa kan ‘ya’yan jam’iyya maza da mata domin cin nasara a babban taron jam’iyyar na 26 ga Maris, 2022.

Wani abin da zai ƙara tabbatar da cancantar Sanata Abdullahi Adamu a wannan kujera ta shugabancin APC shi ne adalcin sa tun a jam’iyyar adawa ta PDP, wanda a kowa ya sani alama ce ta mutum wanda zai kwatanta nagartaccen shugabanci kuma hangen nesa. 

Na yi matuƙar takaicin yadda masu son zuciya da gani a baibai da ke duban waɗanda ba sa son wannan jajurtaccen mutumi a sha’anin shugabancin jam’iyya. A matsayin su ‘yan boko kuma masu ƙwarewa, ina da yaƙinin waɗannan mutane za su mara wa Abdullahi Adamu akan aniyarsa ta kawo cigaba, wanda shi ne mafi dacewa da jan ragamar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

Samun shugaba kamar sa wani abin alfahari ne ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyar, sai dai ire-iren waɗannan mutanen da ke ƙoƙarin bayyana mana son zuciyar su ya fi duk wani abu mai kyau da zai samu jam’iyya da kuma Nijeriya bakiɗaya.

Ba ina nufin Sanata Abdullahi Adamu shi ne kawai mafita da zai magance matsalolin jam’iyyar APC a yanzu ba, amma idan aka kalli manufofin ɗan takara wanda ke son cigaba, mai wanzar da zaman lafiya da kuma ɗinke wata ɓaraka da ta taso, ina ganin ka da a kalli wani face Sanata Abdullahi Adamu.

A matsayin sa na waɗanda suka samar da ita jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu ya fahimci duk wani salon ɗinkewa da mannewa da yi wa kundin tsarin jam’iyyar karatun ta-natsu, tare da sanin duk ɗabi’u da irin halayyar da suka gina jam’iyyar APC akai yayin ƙirƙirar ta.

Ina fatan wani daga duk inda yake, zai ba waɗannan ‘yan APC shawara akan su yi abinda ya dace da zai zama mai kyau ga jam’iyya, saboda dukkan mu mun san yanayin da jam’iyya ke ciki a halin yanzu, kuma mun san abinda zai ɗaga darajar jam’iyya ya kuma ƙara mata karsashi da girma a Afirka, saboda haka, yanzu lokaci ne da za mu cire son zuciya a ɗora mutumin da ya dace da zai ƙarfafa abubuwa a cikin jam’iyya APC. Mai hankali ne kawai zai gane hakan.

Magama ya rubuto ne daga Bauchi, kuma za a iya samun sa ta wannan adireshin na imel [email protected]