Mai Martaba Alhaji Ibrahim Bello: Shekaru bakwai akan karagar Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD

Yana riƙe ne da sarautar Sardaunan Wonaka har zuwa ranar 9 ga Maris, 2015, da Allah ya ɗaga likkafarsa zuwa jagoran Gidan Malam Sambo Ɗan Ashafa, wanda fitaccen almajirin Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo (Muhammad Sambo Ɗan Ashafa) ne ya assasa a shekara ta 1806.

Tun lokacin da aka ƙirƙiro Sarautar Sardauna a cikin tsarin Daular Sakkwato a ƙarni na 19, sannan kuma Sarkin Musulmi na wancan lokaci, wato Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Usmanu Bn Fodiyo, ya naɗa Malam Halilu bin Malam Hassan bin Usmanu bin Fodiyo a matsayin Sardaunan Sakkwato na farko kuma Sarkin Marnona (Marnona a halin yanzu na cikin ƙaramar Hukumar Mulkin Wurno ta Jihar Sakkwato) sai sarautar ta Sardauna ta zamo mai matuƙar girma da daraja a tsakanin ’ya’yan sarauta, musamman a fadojin sarakunan arewacin Najeriya.

Idan ana iya tunawa kuma, Mai Alfarma Sarkin Musulmi na 17, Marigayi Alhaji Sir Abubakar lll, da ƙanensa, Firimiyan Jihar Arewa na farko, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, duka sun riƙe wannan sarauta ta Sardaunan Sakkwato. Hakan ya sa kusan duk wanda ya samu wannan sarauta cikin Ƴaƴan Sarakuna ana kyautata zaton da yardar Allah zaya shiga gidansu a matsayin Sarki a wata rana.

Irin muhimmiyar rawar da Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa ya taka kafin da lokaci da kuma bayan kammala Jihadin da ya yi sanadin kafa Daular Sakkwato ta fi ƙarfin a misalata. Shi ne kuma ya kafa Gusau sannan shine Sarkin Gusau na farko da yayi mulki a tsakanin Shekara ta 1806 zuwa 1827.

Wonaka, wanda gari ne mai matuƙar muhimmanci ga Masarautar Gusau ta yau (inda aka binne gawarsa), yana ɗaya daga cikin wuraren da ya gudanar da rayuwarshi.

Malam Muhammad Bello ɗa ne ga Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Murtala, wanda ya yi sarauta daga Shekara ta 1900 zuwa 1916. Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Murtala, shi kuma ɗa ne ga Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Modibbo, wanda shi kuma ya yi sarauta a tsakanin Shekara ta 1867 zuwa 1876. Shi kuma Muhammadu Modibbo ɗa ne ga Malam Muhammad Sambo ɗan Ashafa, wanda shi kuma ya yi Sarautar Sarkin Katsinan Gusau ne daga shekara ta 1806 zuwa 1827. Cikin iyawar Allah, sai Malam Muhammadu Bello ya samu sarautar wannan gari mai mahimmanci watau Wonaka tare da laƙabin Sarautar “KOGO”.

Kogo Muhammadu Bello ɗan Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Murtala, ɗan Sarkin Katsinan Gusau, Muhammadu Modibbo, ɗan Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Sambo ɗan Ashafa shi ne mahaifin Sarkin Katsinan Gusau na yanzu, Alhaji (Dr.) Ibrahim Bello, wanda Allah ya aza akan karagar mulkin Masarautar Gusau a matsayin Sarki na 15 a ranar Litinin 9 Maris, 2015, wanda kafin hakan shine ya ke riƙe da Sarautar Sardaunan Wonaka.

Ɗaga likafar Mai Martaba Alhaji Ibrahim Bello daga Sardaunan Wonaka zuwa Sarkin Katsinan Gusau shekaru bakwai da suka wuce, bai zama wani abu mai wahala ba, saboda shi mutum ne da ya yi imani da tsarin Allah SWT ta hanyar amfani da ilimin addini da na falsafar rayuwa da ya koya daga Mahaifinsa Kogo Muhammad Bello da kuma Ɗan’uwansa, Sarkin Katsinan Gusau na 8 kuma na 14 cikin jerin wadanda suka yi sarautar Gusau, Marigayi Dr.

Muhammad Kabir Ɗanbaba OFR wanda ya ƙara aza shi bisa tafarkin yin gaskiya da haƙuri da kamun-kai da tsayuwa akan gaskiya da kuma juriya, da uwa uba kuma tsoron Allah. Irin kyakkyawar tarbiyyar da ya samu a gida da kuma ilmin addinin Musulunci da na zamani  da ya samu sun taimaka mishi wajen hidimta wa al’umma. Mai Martaba Alhaji Ibrahim Bello wanda a can baya ya je Kasar Ingila yayi kwas akan sha’anin ilmantarwa akan kiwon lafiya, ya samu nasarori sosai a dukkan wuraren da ya yi aikin gwamnati.

Kama tun daga Shugabancin Makarantun koyar da kiyon lafiya a tsohuwar jihar Sakkwato ( Sakkwato da Kabi da Zamfara ) zuwa muqaman babban sakatare da Kwamishina a Gwamnatin Jihar Zamfara har ya zuwa muƙamin kantoman majalisar Ƙaramar hukumar mulkin Gusau, Jihar Zamfara da ya riqe a lokuta mabanbanta na rayuwarsa ta aikin gwamnati kafin ya gadi gidansu ya nuna ƙwarewa ta musamman akan sha’anin mulki da iya hulɗa da jama’a.

Irin yadda aka yi ta murna da farin ciki a ranar da aka bayar da sanarwar naɗa shi a matsayin Sarkin Katsinan Gusau na 9 daga zuriyar Malam Muhammad Sambo Ɗan Ashafa kuma Sarki na 15 tun daga lokacin da aka assasa masarautar Gusau a shekara ta 1806, ya tabbatar da cikar kyawawan halayen sa da aka bayyana a sama.

Ana iya ganin ɗumbin nasarorin da Mai Martaba Alhaji Ibrahim Bello ya samu cikin waɗannan shekaru bakwai ta hanyar lura da yadda yake tafiyar da mulkin wannan Masarauta cikin kamala da kwarjini da sauke nauyin al’umma gwargwadon hali. Shekaru Bakwai da yayi akan karagar Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa, al’ummar Masarautar Gusau na cigaba da sanya albarka saboda irin cigaban rayuwar mutane da na ita kanta masarautar da ake ta ƙara samu. 

A daidai lokacin da na ke taya Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello murnar cika shekaru 7 a matsayinsa na Sarkin Katsinan Gusau, Shugaban Majalisar Masarautar Gusau kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jahar Zamfara, ina roƙon Allah Mabuwayin Sarki ya qara maka lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

Alhaji Ibrahim Muhammad shi ne Ɗanmadamin Birnin Magaji a Fadar Sarkin Birnin Magaji da ke Jahar Zamfara.
Lambar waya: 08149388442 ko [email protected]
10 ga Maris, 2022