Babban taron APC na kasa: Shinkafi ya janye wa Adamu daga takarar shugaban jamityar APC na kasa

Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau

Kwanaki kaɗan gabanin gudanar da babban taron jam’iyyar APC na ƙasa da za a gudanar a ranar 26 ga watan Maris mai zuwa, jigo a jam’iyyar APC a Jihar Zamfara wanda ke neman kujerar Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ya janye daga takararsa.

Dokta Shinkafi, wanda tsohon Sakataren Jam’iyyar APGA na Ƙasa ne kafin ficewarsa zuwa Jam’iyyar APC tare da Gwamna Matawalle, ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Gusau ranar Talata.

A cewarsa, janyewar tasa ya biyo bayan mayar da kujerar Shugabancin Jam’iyyar na Ƙasa zuwa yankin Arewa ta Tsakiya da aka cimma matsayi, yankin da Sanata Abdullahi Adamu ya fito, inda kuma Majalisar Zartaswar jam’iyyar APC ta Ƙasa ta yi kuma Sanata Adamun ke yin takarar kujerar.

“Ina so in jaddada cewa ina mutunta shawarar da babbar jam’iyyarmu ta yanke na cewa shugaban Jam’iyyar APC a matakin ƙasa zai fito daga yankin Arewa ta Tsakiya kuma a kan haka na janye takarata,” inji Shinkafi.

Idan za a iya tunawa, rahotanni daga Fadar Shugaban Ƙasa na nuni da cewa, Shugaba Muhammadu Buhari na goyon bayan takarar Sanata Adamu ne, kamar yadda jaridu da dama sun wallafa hakan.

Dokta Shinkafi ya ci gaba da nuna cewa, ficewarsa na zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya biyo bayan girmama wa da ya ke yi ga Shugaban Ƙasaasa Muhammadu Buhari.

“Ina so in shaida muku cewa, a yau na yanke shawarar janyewa daga takarar ne a matsayin mutum mai mutunta martabar jam’iyya da shugabannin jam’iyyar tare da mutunta shugaban ƙasa,” Shinkafi ya bayyana.

Ya ce, “Shugaba Buhari ne shugaban jam’iyyar kuma ya dauki matsayi, na sha faɗa muku cewa zan tsaya takara idan har aka sanya shiyyar Arewa maso Yamma, ba na so in yi adawa da abin da shugabana ya faɗa.”

Dokta Shinkafi ya yaba wa duk waɗanda suka mara masa baya a lokacin gwagwarmayar tsaya wa takarar Shugaban Ƙasa, musamman Gwamna Bello Matawalle, Shugaban Riƙo na Ƙasa, Mai Mala Buni, Gwamna Zulum da dai sauransu.

Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da bai wa shugabannin jam’iyyar goyon baya a matakin jiha da ƙasa bakiɗaya domin samun damar kammala babban taron ƙasa mai zuwa cikin nasara da lumana.