Tasirin abokan miji a zaman aure

Daga AMINA YUSUF ALI

Masu karatu sannunmu da sake haɗuwa a wani makon a filin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako muna tafe da bayani a kan yadda abokan miji suke bayar da gudunmowa wajen ingantawa ko kuma rusa zaman aure. 

Mun sani dole ɗan adam ya yi abota a rayuwarsa. Ba ma zai iya rayuwa babu abokan ba. Haka kamar yadda mace ke yin ƙawaye, haka shi ma namijin yana yin abokai. Wasu abokan tare ake tasowa tun ana ƙanana, har  samartaka, duka akan yi tare, har a yi aure.  

To, bayan an yi aure ne kuma, sai kowa ya kama gabansa, haɗuwar ba sosai ba. Wasu har bayan an yi auren kuma suna tare da juna. Wasu kuma abokan karatu ne ko aiki ko sana’a da aka haɗu da su bayan girma. Wasu kuma sai bayan an yi auren ne a ke haɗuwa a ƙulla abota. Wasu ma maƙwabtaka ne inda aka tare, a saba a zama abokai. 

Ko ma dai mene ne, wajen maza, abota na da tsananin muhimmanci. Ba kamar mata ba, akwai tsantsar yarda da aminci a tsakanin maza abokai. Har ta kai ga suna iya gaya musu manyan sirrika na gidajen aurensu, har sukan dogara da ire-iren shawarwarin da abokai suke ba su a gidajen aurensu.  

Bar ta wannan zancen ma, ko kafin neman aure, har ma da lokacin biki dukka abokan ango suna da muhimmiyar rawar da suke takawa. Komai da su ake shawara. Kuma su suke faɗar yadda za a yi. Wani lokacin ma maganarsu ta fi ta amaryar tasiri a wajensa. Kuma saurayi ma yakan rabu da budurwa ta sanadiyyar rashin jituwarta da abokinsa. To wannan kenan. 

To amma tambayar a nan shi ne wanne tasiri waɗannan abokan miji suke yi wajen ginawa ko rusa gidan aure? 

Yadda za mu gane tasirin da abokai sukan iya yi a zaman aure shi ne, sai mu duba waɗanne nau’in abokai ne. Akwai nau’ikan abokai iri -iri. Akwai ɓata-gari, akwai kuma na kirki. 

Kamar yadda masu magana suka ce: “Rai dangin goro, yana buƙatar ban iska a kullum” to haka abin yake. Ba zai yiwu don namiji kawai ya yi aure ba ya tare wajen matarsa kacokam. Yawan zaman taren ma yana jawo a gaji da juna. Gara ya dinga ɗan fita wajen abokai. 

Dole fa namijin sai da namijin. Duk da an ce ka zame wa matarka aboki koyaushe kuna tare. Amma namiji yana buƙatar fita wajen abokai a yi raha, a yi hira irin tasu ta maza. Wasu ma har da wasanni kamar ƙwallon kwando da sauransu. Wasu ma idan sun dawo gida sun ci abinci sun huta, sai su sake ficewa  wajen abokai. Kuma wasu ba sa dawowa ma sai dare ya raba. Amma fa daga wannan ba ragi ba ƙari. Iyakacin nan alaƙar ta tsaya. Domin abubuwa ne da tare da abokan dole za a yi. Ba da iyali ko ‘yan uwa ko ‘ya’ya ba.

Sai dai kuma akwai shaƙiƙan abokai waɗanda sun riga sun zama jiki, waɗanda mutum yake ganin suna da tasiri a rayuwarsa da gidansa waɗannan rukuni su ne mafiya haɗari ga namiji. Domin  su waɗannan rukunan abokan ma har sun fi ‘yanuwa tasiri. 

Maza da dama masu faɗa ne a ji a kan ‘ya’yansu da ƙannensu har ma matansu. Suna kula da na ƙasansu sosai har ya kai ga suna hana su hulɗa da abokan banza domin gudun gurɓacewar tarbiyya. Ba tare sun gano cewa su kansu za su iya afkawa tarkon abokai ba. Abinda yawancin mata suka gano a kan maza shi ne, (a gafarce ni) suna matuƙar satar amsa a rayuwar aure. Maza ƙalilan ne tsayayyu suke iya tafiyar da rayuwar gidansu ba tare da dogaro da shawarar abokai ko danginsu mata ko maza ba. 

Hakazalika, mugayen ɗabi’un maza a wajen abokai suke koya. Ƙin dawowa gida da dare, shaye-shaye, wulaƙanta mace, neman mata, duk dai. A hankali namiji yake koya wajen abokai ko da kuwa ba halinsa ba ne. Ka ga kenan yana da kyau ba matarsa ko yaransa kaɗai ne ko ƙanne suke buƙatar saiti ba, kai ma da kanka kana buƙatar saiti da shiriya daga muggan abokai. 

Kuma ra’ayin al’umma a ƙasar Hausa yana matuƙar taimakawa. Kamar yadda kullum ake cewa mace wai namiji ba ɗan goyo ba ne, haka shi ma namijin ake zuga shi game da mace.

Tun bai san matar da zai aura ba ya riga ya gama wassafa yadda take da ma yadda zaman nata zai kasance tare da shi. An riga an yi masa karatun mata a ƙwaƙwalwarsa ya haddace a kansa. 

Haka abubuwan da suke faruwa gidan abokansa da matansu, musamman ma marasa daɗi su ma suna nan ya adana bidiyonsu a ƙwaƙwalwarsa. Sannan kuma bugu da ƙari, ga haddar yadda ya taso ya gani a gidansu ana rayuwa, duk wannan haddar fa ba za ta gogu ba. To yaushe kuwa za a zauna lafiya? 

Maza da dama waɗannan abubuwa da na zana a sama musamman abokai su ne makarantarsu ta farko idan sun shiga gidan aure. Ba su da lokacin da za su zauna su karanci matansu har su fahimci juna. Su dai sun dogara daga waɗancan karatun da suka yi tun a baya. Duk irin uƙubar da gallazawar da abokansa suke sha a wajen matansu, da irin rashin zaman lafiya, ke ma jira yake kawai hakan ta faru tsakaninki da shi.

Kullum sa ran haka yake yi. Kuma dukkan laifukan da matan abokansu suke yi da rashin kyautata musu shi ma jira yake yi ke ma ki yi masa ya yi miki irin hukuncin da abokansa suka gaya masa suna yi wa matansu.

Shi ya sa sai a yi aure ki kasa gane kan namiji da gindinsa. Ko ya daina yi miki fara’a yadda kuke a waje kafin ku yi aure, sai ke ma ki hau. Da ma ke ma wataƙila an riga an zuga ki. Ina za a zauna lafiya? Ke duk kina ta faɗa da mijinki wanda ya kamata a ce haɗin kai ne tsakaninku don gina rayuwa mai ɗorewa. Amma shi kin kasa gane kansa. Sai a fara zancen ko jifa ne, ko danginsa. Sam! Kawai yana yi wa matarsa hukunci ne da laifukan da matan abokansa suke aikatawa. 

Amma Yayana ka tava zama ka yi tunanin cewa, ko a ɗakin mahaifiyarka ‘yanuwanka mata da ta haifa dukkansu halinsu ɗaya? Kowacce yadda take rayuwa da ku da kuma mijinta ɗaya ne? To idan ba ɗaya ba ne, ya za a yi matar abokinka da matarka su zama masu hali ɗaya? 

Ka tuna fa, wajen da ka je ka ɗauko matarka daban, wajen da shi ma abokinka ya je ya ɗauko tasa daban. To me ya sa za su cancanci zato iri ɗaya da hukunci iri guda? Sai ka yi ƙoƙarin sanin wacece matarka da kyakkyawar zuciya ba tare da ka auna ta a sikelin wasu matan ba. Matarka matarka ce, matar abokinka matarsa ce ba haɗi. Ka gane haka, sai ka ga ka zauna lafiya. Maza da yawa ba su gane cewa kaso mai yawa na farin cikin da za su iya samu a rayuwarsu yana da alaƙa da matansu ba. Idan ka samu kyakkyawar alaqa da matarka za ka samu kwanciyar hankali a matsayinta na abokiyar rayuwarka. Sannan kuma zaman aure sai kuna wa juna uzuri. Tunda dukkanku ‘yan Adam ne, ba mala’ika ko sahabi ko ma’asumi a cikinku. 

Kuma kada ka manta, kai ma fa yadda abokai suka yi maka famfo cewa, mata ba su da kirki, ita ma fa haka ta tashi tun tana ƙaramar yarinya da aƙidar cewa, namiji ba ɗan goyo ba ne. Ita ma yadda kake jiran laifinta da rashin kirkinta kafin ta aikata, kai ma haka take tsammani daga gare ka. Abinda zai kwance wannan ƙullin zaton dake tsakaninku shi ne, ka canza mata tunani. Abinda take tsammani ta ga ka yi saɓanin hankalinta. Hakan shi ne zai sa aminci da yarda da girmamawa ya ginu a tsakaninku.

Haka ita ma matar ya kamata a ce kin san halin mijinki. Kuma daga ya yi wani abu da kika san ba ya cikin halayensa, bincike za ki yi ki gano matsalar. Mijinki ba abokin gabarki ba ne. Kuma idan kin san halinsa kika ga ya yi wani abu, to ki bincika ki gani. Wataƙila zuga ce. Kuma kada ki yi saurin hasala, saboda zai ƙara tabbatar da abinda yake gani da jin labari wajen abokansa. 

Kai kuma Yayana, kamar yadda ka san cewa akwai abubuwa da dama waɗanda za ka iya yi tare da abokai bai shafi ɓangaren iyali ba, to fa su ma iyalin akwai wasu keɓantattun abubuwa da ya kamata a ce ka keɓance tare da su. 

Hakazalika, ba kowanne sirrin gidanka ya kamata aboki ya sani ba. Idan matsala ta qi ci da cinyewa me ya sa ba za ka zaunar da matarka ku sulhunta ba? Idan kuma abu ya ci tura, ai akwai iyaye. 

Sai dai kuma abokan ma fa ba a taru an zama ɗaya ba. Akwai abokanai na amana waɗanda ko me za a yi za su faɗa maka gaskiya a kan abinda kake yi, kuma su ma su ba da shawara ta gari wacce za ta amfani abokin nasu.

Sai dai su irin waɗannan abokan ba su da yawa, kuma ba su da tasiri sosai saboda su za su faɗi gaskiya mai ɗaci ne. Ba lallai ne kuma gaskiyar abokin ya ji daɗinta ko ya amshe ta ba. Saboda ba lallai a goyi bayansa ko ra’ayinsa ba.

 Akwai abokai kuma masu shisshigewa. Waɗanda ko ana so, ko ba a so, sai sun cusa kai a cikin zaman auren abokinsu. Su suke ba da muguwar shawara su ɗora abokansu a kan turbar gan-gan ko keken ɓera. Domin su wannan muguwar shawarar da ba za su iya aiwatar da ita a gidajensu ba. Wasu  da yawa ma za su iya cika maka baki, kuma ba na raba Allah biyu, ƙarya suke yi. 

Kuma abin lura ma a nan shi ne, kowa  da matsalar da ta dame si, mai ɗaki shi ya san inda ke masa yoyo. Duk wanda zai ta tunzura ka ka ƙi zaman lafiya da iyalinka yana ƙwararka ne. Don shi ba lallai ne hakan yake a gidansa ba. 

Kuma ba cewa aka yi magidanci kada ya yi abokai ba. Amma abokai su zama kawai dai a abokan. Ba masu tsomo baki a rayuwar aurenka ba ne. Musamman irin waɗancan ɓata-garin da aka bayyana a baya. Abokai rahama ne sosai a rayuwar mutum. Domin suna matuqar tallafa maka a rayuwa.

Kamata ya yi harkarka daban da su, gidanka ma daban. Shigar da xaya cikin xaya yana haifar da matsala. Kuma sannan idan za a yi zaven abokai a zavo na gari. Waxanda za ku bi tafarkin da ya dace. Domin ko ba daxe, ko ba jima, mutanen da kake tare dole halayensu su nashe ka, ba tare da ka sani ba. Wani ma fa son abin hannunka ne zai sa shi ya yi ta yi maka famfo don ganin abubuwa sun cave maka a gida ka y ta nemsn shawararsa.

Kuma ko abokin kirkin su ma ba komai za a iya gaya musu ba. Ai sirri yana da muhimmanci a rayuwar aure. Ba komai ma’aurata za su dinga faxa wa ‘yan waje ba. 

Ke matar aure ki sani, abokai suna da matuqar muhimmanci ga rayuwar kowa, amma idan na kirki ne. Abokai da yawa kan zama silar arziki da xaukakar abokansu. Kada ki ta da hankali a kan abokan miji, in dai ba wata varna ko illa mabayyaniya kika gani ba. Kuma dole wai abin, sai namijin. Kamar yadda ke ma wasu a ububuwan ba lallai sai kin yi da mijinki ba. Kina buqatar qawayenki mata ku yi tare. To shi ma namijin haka ne. Ba za ki iya taka masa rawar matar aure da ta aboki a lokaci guda ba. 

Kai kuma aboki ka duba Allah ka duba Annabi ka sani aure sunnar Annabi (SAW) ne. Kuma tsakaninka da abokinka amana ce. Wani ko matarsa ko danginsa ba ya sirri da su sai kai.  Ka ji tsoron Allah ka yi zuga da shawarwari mugaye da za su jawo ya rushe ko a samu tazgaro a zaman aure. Ka sani idan ka taimaka wajen ƙarfafa shi, to za ka samu lada maras misaltuwa tare da samun albarka a rayuwarka. Ko ba a harkar aure ba, akwai abokai sosai da suke yi wa abokansu yankan baya da cin amana. Wani ma ya hana shi cigaba a rayuwa. Allah dai ya haɗa mazaje da abokan kirki. Allah ya haɗa mu a wani makon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *