Tattaki a yanar gizo: Leƙe cikin zaurukan YahooGroups

Daga KHALID MUSA

Mahawarar Ruwa
Kafin ɗaurin ɗamba, Ina son masu sauraro na su sani cewa, wannan muƙala ba nazarin ilmi ba ce (Academic Presentation). Don haka ba lallai ne ta cika dukkan ƙa’idojin nazari a tsarin darasin harshe ba. Wannan takarda nazari ce kawai ta mai sha’awar adabi da bibiya. Na kauce wa bayar da tarihin taurarin muhawarar, haka nan ban yi izna da kawo fassarar wasu jigogin kalmomi ba, domin larurar da na ambata a sama da kuma kauce wa tsawaitawa. Ina fata za a lura kuma a yi min uzurin dukkan wata gazawata da ka iya bayyana cikin wannan takarda abar gabatarwa.

Dandalin sada zumunta na YahooGroup
Gabannin yawaitar wuraren hira da tattaunawar kafofin sada zumunta irin su Facebook, Whatsapp da sauransu, dandalin sada zumunci na yahoogroups shine wurin da ya yi fice kuma ya tara masana da manazarta domin musayar ra’ayi da tattaunawa. Muna da zaurukan da su ka shahara a tsakanin marubuta, manazarta da masu sha’awar adabi kamar haka:

  1. Dandalin Marubuta
  2. Dandalin Masoya
  3. Majalisar fina-finan Hausa
  4. Dandalin Hausa da Hausawa da kuma
  5. Dandalin Mawaƙan Hausa
    Sai dai a cikin wadannan zauruka, ukun farko ne su ka fi sharafi wajen muhawarorin da su ka ja hankulan mahalarta da dama. An tafka muhawarori a wannan zamani ma su matukar jan hankali gaya gami da kayatarwa. Dalilin wannan rubutu nawa shine don na gayyaci ma su sha’awar adabi zuwa wani tattaki don leƙe cikin irin muhawarorin da waɗannan zauruka su ka haifar.

Zan fara ne da Muhawar Ruwa wacce Malam Bello Muhammad Ɗanyaya Editan Makarantar Hausa ya haifar da ita a cikin shekarar 2011 Ranar Laraba 22 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 11:16. A ranar wannan muhawara, an wayi gari cikin ruwa kuma a ka wuni cikinsa. Makarantar Hausa ya buɗe muhawarar ne da wasu baitika huɗu masu dango bibiyu kamar haka.

  1. Allah ruwa Allah ruwa amma kadan
    In sun wuce haka Rabbu za mu yi kuka.
  2. Allah katanginmu duk sun sunkuya
    In sunka kai ƙasa za mu koma bukka.
  3. Ambaliya mun sha ta Allah Ka sani
    Har ma manoma ba su ƙaunar shuka.
  4. Allah muna so ba mu cewa ba mu so
    Amma a yo su kaɗan-kaɗan ba duka.

Honey Asal wanda ya fi shahara da sunan Habibiy a waɗannan zauruka shine ya fara buɗe shafin Muhawarar da ta’aliƙinsa wanda yake martini ne ga Makarantar Hausa da yake ganin ruwa yayi yawa kuma akwai buƙatar a roƙi Allah tsagaitawarsa. Wannan Ta’aliƙi na Malam Habibiy ya zo ne cikin baituka biyar bisa wazanin da Makarantar Hausa yayi amfani da shi kamar haka:

  1. Allah ruwa ka zubo da su mai yawa
    Ba mu kosawa da yawan albarkarka
  2. Makarantar Hausa ya koka a tsaya haka
    Afuwa, Rabbi Ubangiji muna rokonka
  3. Ruwa kamar an zubar da bakin kwarya
    Allah dado mana mai yawan albarka
  4. Ni’imarka muke bida ba mu wadatuwa
    Idan ta takaita Jallah sai mu zan mun koka
  5. Ruwa, Allah ruwa zubo mana shi mai yawa
    Zubar mana ba cutarwa Rabbi gare ka makoka
     
    Waɗannan baituka guda tara jumlatan sune su ka buɗe wannan gagarumar muhawara da aka tafka ta har ta jawo hankalin wani ƙwararren marubucin waƙa mai Suna Bashir Muhammad Idris. Malam Bashir ya ƙalubalanci Makarantar Hausa cikin baituka talatin waɗanda ke cike da Hikima da ƙwarewar iya saka zaren waƙa. Ya fara da cewa ai sam ruwa ba ya yawa, abu mafi muhimmanci a roƙi Allah ya bayar da mai albarka. Ga Malam Bashir, ba a jingina rashin albarka ga ruwa ko da ya yi ɓarna. Muna iya fahimtar ra’ayinsa inda yake cewa:
  6. Koda ruwan sama anyi ya rushe gida
    Lallai akwai ni’ima ciki ba shakka
  7. Domin idan mun roƙi ai yo ɗan kaɗan
    Me zamu ba tsirrai da kayan shuka?
  8. Roƙon ruwan fa muke tayi in babu 
    Harma fari kan faru dan ba shuka
  9. Kai dai mu roƙi Tabara yalwar arziki
    Domin mu huta ginin kago ko jinka

Ya yi amfanin da salon kwatance dan nusar da ra’ayinsa tare da nuna cewa nahiyarmu a taswirar duniya ba mu da yanayin da za mu koka game da balahira ko musibar ruwan sama. Ya kawo wasu nahiyoyi domin aunawa da abinda yake abkuwa a tamu nahiyar kamar haka:

  1. Wata nahiyar ko ruwan (Flood) ke sauka
    Su rai sukewa basu zancen shuka
  2. Ka ga ga gida ya zam kamar jirgin ruwa
    A saman ruwa juyi yake yana fanka
  3. Mu ma yi raki kan yawan samun ruwa?
    In yai yawa ka gayan ina jirginka?
  4. Ballantana ma har kace yai ma yawa
    Ambaliya na murkushe gonarka
  5. Da kadan a guna gwara mai tarin yawa
    Amma fa banda yawan da zai kashe shuka
  6. Na gane kan adu’ar da kai na gamsu tsaf!
    Ni dai kawai rokon “kadan” naka shakka

Ɗaya daga cikin taurarin wannan Muhawara wato Malam Habibiy yayi amfani da salon zuga da tunzurarwa tsakanin Makarantar Hausa da Bashir Muhammad Idris, sannan ya nuna mana tsananin ruwan da zamanin da ya ɗauka gami da halin takurar da aka shiga musabbabin yawan zubarsa ba kakkautawa. Ya bijiro da wadannan hasashe cikin baituka goma sha tara. Za mu iya ganin tsokacinmu cikin waɗannan baitukan:

  1. Bashir ka yi bugu bugun ya ƙarfafa
    Da an ki da an so sunkuye a gareka
  2. Ruwa tun talatainin daren jiya
    Har a yanzu talatar Rabbuka
  3. Mun zaune gidajenmu ba fita
    Mun jangwame zaman hira zauruka
  4. Ya je ya dawo ba ya ko jira
    Yau ina tsawon zamanmu a zauruka
  5. Makaranta ruwa kam yai yawa,
    Amma ina gaminsa da dufanuka
  6. Daren jiya har a yau wayar gari
    Cikin ruwa muke tsundum ba harraka
  7. Mamman Bashar dan Idrisu gagarau Kana daka ne ko can gonataka.

Da alama ziga-zigin da Habibiy ke hurawa tsakanin Makarantar Hausa da Malam Bashir yayi tasiri sosai. Domin Makarantar Hausa ya sake yunkurawa tare da yin martini ga Malam Bashir Idris. Ya nuna amincewarsa da kwarewar Malamin tare da tsayawa kan bakansa na yawan ruwa da neman a tsagaita shi cikin wadannan baituka:

  1. Ya kai gwani Wallahi kowa ya gani
    Ya tsara waka ya kashe mani lakka.
  2. Sai dai kawai ya nuna ba shi da tausayi
    Shi ne ya sa na fito ina ‘yar shakka.
  3. In dai ruwa bai yin yawa Dufanu fa?
    In bai yawa mis sa yakan hana harka?
  4. Baitinsa dai ne zai hana mani rantsuwa
    In ce kure Wallahi yau na tafka.
  5. Baiti guda ne ga shi nan Honey kasa
    Zance guda ne ni da shi muka ba ka.
  6. Na ce ruwa amma kadan shi ko ya ce
    Amma fa banda yawan da zai kashe shuka.
  7. Na so a ce ya tausasa ya tausaya
    Ya roki sauƙi gunmu don Mai Makka.
  8. Mun sha wuta mun sha ruwa duk ya sani
    Sannan muna bisa shan bala’in iska!

A cikin baituka goma-sha-biyar Malam Bashir ya mayar da martaninsa ga Makarantar Hausa. Ya ƙalubalence shi bisa kwatance da Ruwan Dufanu don nuna cewa ba kowane ruwa ne ke zama ruwan albarka ba.

  1. Kace ruwan Dufanu kai! barkanka!
    Karma ka soma kwatanta wanga da naka
  2. Wannan ruwan nuni yake da azaba
    Dan gargadin dukkanmu ai yassauka
  3. Kuma duk yawan dufanu in ka duba
    Mabiya Nuhu sun tsallake ba shakka
  4. Zancen ruwan Dufanu bai taso ba
    Magana muke ta yawan ruwa a garinka
  5. In banda zancen editan makaranta?
    Ai dole inda ruwa a dakata harka
  6. A ce kawai wai dan ruwa zai sauka
    Duk sai mu hau sababi da yamutsa fuska? 

Masu muhawar sun nuna dattaku da fahimtar juna bisa kalubalen da ke gudana a tsakaninsu. Makarantar Hausa ya yabi Malam Bashir Hakanan shima Malam Bashir ya yabi Makarantar Hausa tare da nuna cewa dukkan wannan muhawara ya fa fahimci an kawo ta ne domin wasa kwakwalwa. Kasancewar dukkan taurarin Muhawarar na haduwa ne kawai a yanar gizo, sun nuna kwadayin sanin juna kamar yadda waɗannan baituka su ka nuna:

  1. Ko babu komai kaga kai mana washi
    Washin ƙwaƙwalwa mun yi kan wakenka
  2. Kuma ga su honey na dada mana kaimi
    Duk dai da ba ka so musan sunanka
  3. Honey Asal fa ka ce ka kara Habibiy
    A cikinsu wanne wai ainihin sunanka?
  4. Zan dan tsaya haka dan inje in rintsa
    Haka nai rubutun in gyangyada in farka

Daga wannan gaba kuma sai muhawarar ta fara sauka daga bigirenta ya zuwa wani wadi da ya shafi khususiyyarsu. Farkon faruwar wannnan juyin shine saukowar Makarantar Hausa gami da karbar rinjayen Bashir Muhammad Idris bisanshi cikin wannan jayayya mai kayatarwa.

  1. Zauna ka futa tunda ka zama gagarau
    Bai warwara yadinka in ka dinka.
  2. Kwanta ka huta tunda ka zama kandamau
    Bai girgiza tulunka in ka girka.
  3. Na dauki wakata da taka na gwargwada
    Na gano wakar taka kyau ta ninka.
  4. An dai gwada an san mawakin gaskiya
    Shi ne Bashir lambar yabo ya dauka.
  5. An dai gwada an san mawaƙin Hausa yau
    Mu masu kauna tai mu yo masa barka
  6. Mallam Bashir sannunka sannu da ƙoƙari
    Sai mun haɗe wataran a kan wata harka
  7. Ai kai Bashir na ma saki ma tun jiya
    Kai ne uba na yarda na zama jika.
  8. Na sunkuya na durƙusa na sallama
    Ba Bello ma balle ya ce ya fi ka!

Da waɗannan baituka Makarantar Hausa ya fice daga wananan Muhawara abinda ya kawo karshen Maudhu’in da ake fafatawa a kansa. Cikin tawali’u gami da Kankan da kai irin na Malamai masu gudun kambamawa, Malam Bashir ya mayar da martanin wannan mika wuya da Makarantar Hausa yayi kana ya bayar da hisabin baitukansa a wannan muhawara a kan Ruwa kamar haka:

  1. Wai kaji ni za a wa kofarraggo
    To naki wayan so kake in afka
  2. So dai kake ka zugan in doshi aradu
    In ta taho kayi wuf! ka kama gabanka
  3. Halinku Malammai sarai na sanshi
    Ku baku san girma ace kun ɗauka
  4. Sam bani yarda ni ka dauran gurmi
    Na yarda dai dauran dakon gafakaraka
  5. In zamma mai sharar cikin zaurenka
    Ko mai dakan ‘karo gami da zigenka
  6. Watarana sai kaga na zamo wani gardi Titibiri dan yanzu nakke a wajenka
  7. Waken da kai ne tun da farin farko
    Shaukin sa ne yassani sai da na tanka
  8. Dan naga waka tayi waka Malam!
    Tamkar Alu dan sidi yarraineka
  9. Mai illimi ai shi ka ɗaukar gyara
    In an gaya masa take har ya ɗauka
  10. Nai baitika arba’in da biyar da
    To sun zamo sittin a jimla dukka.

Shigowar Malam Fatuhu Mustapha cikin Muhawar ne ya sake yanke ta dungurum daga Muhallinta sai batun ya koma kokarin kambama juna da kuma bara irin ta Malamai ko almajirai. Sannan muhawarar ta sauka daga bin tafarkin tsarin da a ka dauko ta. Misali a can baya dukkan taurarin muhawarar na tafiyar da ita ne a bisa wazani guda tare da tsayawa a kan kafiya guda daya amma Malam Fatuhu ya cire ta daga wannan tsari ya zuwa zubin Ballagaza. Sai dai kuma duk da hakan sauran taurarin ba su fita daga wancan tsari da zubin da suka tawo da shi ba tun farko. Ga yadda Malam Fatihu ya tsirgo cikin Muhawarar:

  1. Ni wagga baiti na Manyan Malamai Ya Jahili zai gane yadda ka yi su,
    Na roki sarkin nan da yai
    Ya sa ku yarda insha kadan a gurinku
  2. Kai ka ji baiti sai kace harsashi
    Wani na fitar tsawa kama da aradu
    Har ka tuna min Audun Gwandu Sha’iri
  3. Ko ko Aliyu Namangin Zariya
    Sai najji tamkar Shitu dan Abdurrahman
    Ni na za ta Suka na da rai bai kau ba. 

Cikin Tawali’u irin nasa, Malama Bashir ya amsa wa Fatihu wannan yabo da ya yi:

1.Turƙashi yau na sai ruwan dafa kaina!
Na tsokano su giji giji kan waka

  1. Na tsallaka gonar su Malam Fatuhu
    Na tuba Malam bani ja da irinka
  2. Na sha karanta kala kalar wakenka
    Da ka sassaka kan internet shafinka
  3. Sai godiya mun amshi taka gudun mawa
    Allah ya saka mun yaba da nufinka.

Haka dai su ka ci gaba da irin wannan salo har ya zuwa inda Malam Bashir ke kai bukar sa ga Malam Fatihu ta neman ya taimaka masa da wata waƙar Aliyu Namangi a wani baitinsa inda yake cewa:

  1. Ga tambaya dama ina so zamma
    Wakar Furan gero nake so gunka
  2. Wakar furan geron Aliyu Namangi?
    Na san akwai su dami dami taskarka
  3. Dan na karanta dayar da yaiwa ‘Keke’
    Can kwanakin baya na ganta agunka
  4. To, in akwaita ina bara da a bani
    Na roki alfarma ina dakonka.

Shi kuma Malam Fatihu ya amsa masa da cewa:

  1. A batun Aliyu na Mangi babban
    Wakar furen gero ina kawo ma

Wannan kalma ta Furen Gero da Malam Fatihu ya yi amfani da ita a matsayin sunan littafin waƙar Malam Aliyu Namangi ya so ya sake tayar da wata kurar mahawarar inda Malam Habibiy ya ke tuhumar daidaiton Kalmar da kuma neman ba’asin ma’anarta, cewa shin Fura ce ko Fure? Malam Habibiy ya sak’a wannan tuhuma kan fahimtar matsayin fure ga gero tare da amfanin da al’adar wasan Kanawa da Zage-Zagi.

  1. Tambaya nake ya sahibi baharunmu
    Ya kai dan Idrisu tinjimin albarka
  2. Gero da fure cikin furanni anya?
    To, ya furen gero yake a saninka?
  3. Namangi mai waken furar gero take,
    Koko furen gero cikin taskokinka?
  4. Fura ga gero abar sani a garemu
    Amma fure na yi jim ina yin shakka
  5. Huda ga gero ce ke amsa sunan fure?
    To ina bununu can a Lugar yarenka
  6. Namangi Bazazzagi ne kun jiya,
    Rakaka can ga Zazzau ne duka.
  7. Ba na musun suna ga shi littafi na sa,
    Lahajar yare nake bidar fatawa ta ka,
  8. Gero ga Zazzau ba yawa to ka jiya,
    Ya Namangi zai san Bununu a zato na ka?
  9. Ijiya a Zazzau idanu ne ka ji fa,
    Kano ka ke ko ko Zazzau ka za ka?
  10. Babawan Zazzau yayi Baubauci nasa
    Gare shi rigar kaya Hausa in har ya saka,
  11. Malam Aliyu Namangi Hasken Zariya
    Allah ka gafarta masa don girma na ka.

A nan wannan Muhawarar ta tuke domin Malam Fatuhu bai tanka ba illa wadannan kalmomi da ya rubutasu ba a zubin waka ba “Malam haka sunan littafin yake. Haka Namangi ya rubuta.”

A ƙarshe za mu lura cewa:

  1. Taurarin Muhawarar ba dukan su ne ke da masaniyar juna ba a zahiri illa haduwarsu kawai a dandalin yanar gizo, duk da dai cewa akwai alamar sanin juna tsakanin Malam Bashir Muhammad Idris da Malam Fatuhu Mustapha.
  2. Baitukan ma su muhawarar yayi mana manuniyar zurfin nazarinsu cikin wasu ilmuka, kamar harshen Larabci, ilmin Jogurafi, Tarihin kasa da al’umma, harshen Inglishi, da kuma kwarewarsu cikin harshen Hausa duba da yadda suke sarrafa harshe cikin baitukansu yadda su ka so.
  3. Da alamun masu Muhawarar ba yara ba ne a badini domin baiyanar manyance cikin baitukansu da nuna sanin ya kamata. Sun yi Muhawarar cikin tsafta babu nuna Isa ga kuma Kankan da kai.
  4. Lahjar harshen Taurarin cikin baitukansu ya nuna nahiyar da suka fito, muna iya gane Bello Muhammad Danyaya mai yiwuwa daga yankin Sakkwato ya ke domin yawaitar nason Hausar Sakkwato cikin baitukansa ba tare da larurar waka ce ta jawo hakan ba, yayin da sauran masu muhawarar sun fito daga nahiyar Kano ce.
  5. Haka nan muna iya lura da cewa dandalin sada zumunta na Yahoo a waccan lokaci ya taka rawa muhimmiya wajen bayar da damar habaka Adabin Hausa ta hanyar samuwar irin wadannan Majalisu.
  6. Tun tuni akwai ma su kaffa-kaffa da yanar gizo wadanda ba su saki jiki da ita ba, hakan ya ke sanya su boye haƙiƙaninsu kamar Malam Habibiy wanda adireshinsa na yahoo ya bayar da sunansa a matsayin Honey Asal, har wayau ban sami sanin haƙiƙanin ko wanene shi ba.
    Tammat!