Tinubu bai cancanci shugabancin Nijeriya ba, inji Abubakar Billy, jikan Tafawa Ɓalewa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

A kwanakin baya ne dai, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, a cikin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Chanels, ya yi tsokaci da cewar, akwai wasu jami’ai dake cikin Fadar Shugaban Ƙasa waɗanda ba su so Tinubu ya kasance ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC ba. Ya ce waɗannan mutane suna yin bultu don ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi abinda ya dace. El-Rufa’i ya ce, “akwai wasu gungu a fadar shugaban ƙasa da suke yin da’awar mu faɗi zaɓe.”  Wakilin Blueprint Manhaja na daga cikin wasu manema labarai da suka yi hira da jikan Marigayi Firimiya Sir Abubakar Tafawa Balewa akan wannan batu. Ga yadda hirar tasu ta kasance:

Ko mene ne ke tafe da kai?

Sunana Abubakar Billy Tafawa Balewa, xan Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi. Mun zo kamfen ne na ɗan takarar gwamnanmu na Jihar Bauchi, Maigirma, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, Ƙauran Bauchi, kuma a cikin zagayawa da yake yi, yanzu mun zo nan ƙaramar hukumar Tafawa Balewa ne, ƙaramar hukuma ta goma sha shida kenan da muke zagayawa da shi, inda yake yin kamfen ta neman sake komawa wa’adin mulki na biyu wanda zai fara a watan Mayu na wannan shekara ta 2023.

Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi wani fashin baƙi, inda yake gani kamar wasu daga cikin fadar gwamnatin tarayya suna zagon ƙasa wa ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. yaya ka kalli irin waɗannan kalamai na Gwamna Nasir El-Rufa’i?

Ni a gani na wannan abin ya zama fargar jaji ne, ai dattaku ba shekaru ba ne, yana cewar, shekarun sa zai kasance sittin da huɗu, wai shi ma ya zama dattijo, dattaku kuwa ba shekaru ba ne, hali ne. Waɗannan dattawan Arewa da ya kira su sunayen da ya kira su, dukkansu kowanne ba wai don sun riƙe kujerun gwamnoni ko ministoci ba ne suka zama dattawan Arewa, sun zama dattawan Arewa ne saboda muradun Arewa da suka kare na tsawon shekaru da suka tsaya akai.

Yau idan ba don irin ƙoƙarinsu da hangen nesan su ba, suka yi tabbacin dole sai wani ɗan Arewa ya tsaya takara, da yanzu fa wata magana daban muke yi, da yanzu ƙilan takarar ana yi ne a tsakanin Bola Ahmed Tinubu da kuma Nyesom Wike, amma a bisa jajircewarsu suka yi hangen dole ba doka ba ce dole sai ɗan Kudu ne zai yi takara, Arewan ma su fitar da ɗan takara, suka kuma fito da ɗan takara wanda shine Maigirma Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar.  Yau har su Nasir El-Rufa’i suna ganin faɗuwa ce a gare su, suka gani ƙarara, kuma mu a wurin mu Buhari ya gama mulki, domin shi Buhari sau nawa zai yi mulkin Nijeriya ɗan Arewa da ɗan Nijeriya za a zaɓe shi, amma yanzu ya gama, kuma kada ya sanya baki a cikin lamarin ko wane ne zai yi shugabanci, ko kuma ya gwada ga inda zuciyarsa ta dosa ta yadda ‘yan Nijeriya za su ba shi martaba da mutuncin da ya dace da shi, idan an yi zaɓe babu wata almundahana ko carafke ko satar ƙuri’u, kuma aka bai wa wanda ya ci zaɓe. Shi Gwamna Nasir El-Rufa’i, shi Atiku Abubakar ya ɗaga hannunsa shekara ta 1999 aka ba shi Darakta Janar hukumar sayar da kadarorin gwamnatin tarayya (BPE), kuma ya sanya aka ba shi kujerar minista.

Amma daga baya me ya yi wa Atiku, cin mutuncisa ya yi, ana taro a gaban Obasanjo, aka zuga shi Nasir El-Rufa’i ya ce wa Atiku ya fita daga taron lokacin ana kishishiyar tazarcen Obasanjo, mene ne ba mu sani ba, kuma ma El-Rufa’i malalaci, matsoraci wanda da zarar sun faɗi zaɓe, gudu zai yi ya bar Nijeriya, mu mun san ire-iren take-takensu, faɗuwa suka gani ƙarara ya taho masu, kuma idan Allah ya yarda wannan yaudara da suka nemi su yi Arewa wai Musulmi da Musulmi, wani wai shi Tinubu shine ya haɓaka Legas, sun san duk ƙarya ce tsagwaronta, ƙarya ce ƙarara.

Ka sanya su biyun nan, Atiku da Tinubu akan sikeli, ka gwada ka gani wane ne zai fi wani kyautata wa Nijeriya ko kyautata wa Arewacin Nijeriya?

To, yaya ra’ayinka ko ra’ayin ku yake?

Mu mun bar wani maluƙi ya zo ya yaudaremu, su waɗannan su suka kai mu inda suka baro, dawa-dawa suka yi shawarwarin da suka fito da Tinubu, waɗannan gwamnonin Yamma maso Arewan da suke faɗi, suke maganar sun zauna sun ɗauki matsaya, dole ne a yi Tinubu, babu dole, babu wanda zai sauraresu.

Babu wani alƙawari da aka yi da Tinubu, amma ya bayar da gudummawa sosai wajen zuwan Buhari, kamar yadda wasu mutane daban-daban masu yawan gaske suka bayar da tasu gudummawar, amma ba dole ba ne a ce shi Tinubu shine zai tsaya takarar shugabancin ƙasa. Idan cancanta ma ake nufi, wai lokacinsa ya zo, ya kai Atiku ne cancanta ne, Atiku ya yi takara da Abiola ya bar masa, tun yaushe shi ma yake yin takara, in dai cancanta ne da gogewa a nema ko tafiyar da shugabancin Nijariya, ai Atiku ya fi Tinubu tagazawa da shiga takarar shugabanci. Tinubu yana cewa wai lokacinsa ne yanzu, saboda gudummawa kaɗai da ya bayar, mutane nawa suka bayar da tasu gudummawa, gudummawa an bayar da shi babu iyaka, kuma akwai hanyoyi da za a iya taimaka masa, kuma an taimaka masa a cikin wannan gwamnatin, kusan da farkon gwamnatin Buhari, duk ba ‘yan Kudu maso Yamman ba ne suka mamaye gwamnatin ta Buhari da manyan muƙamai, kuma me yake nema ko yake so a yi masa, lalle ne sai an ba shi shugabanci, shugabancin Nijeriya ya wuce waɗqqan koyo.

Ina mafita take?

’Yan Arewa su fito su yi wa kansu ƙiyamullaili, siyasar Nijeriya ta canja, ba irin ta shekaru aru-aru da suka wuce ake yi ba. Mu na yin siyasa, ka na kallo ‘yan Kudu maso Gabas suka fito da ɗan takara, har wata jam’iyya suka ɗauka, suka fito da nasu ɗan takara, su ma Kudu maso Yamma sun fito da nasu ɗan takara, mu ma Arewa ga namu, dole ne a tsaya babu kuma wani kundin tsarin mulki na ƙasar nan da yace wai sai ɗan sashi kaza ba. Ga namu nan, Atiku ne namu, idan cancanta ne da gogewa, ya fi duk sauran gogewa, El-Rufa’i yanzu ya ga faɗuwa ce a gaban su zai kawo mana wani ɓangaranci, ko tikitin Musulmi da Musulmi, mu duk ba za mu bi wannan yaudarar tasa ba, bayan mu ‘yan Arewa, an san mu da gogewa da fahimtar siyasa da wayewar siyasa. Wallahi, wallahi, wallahi ba za mu yi tumun dare ba, sun kawo mana dodon bango, ba za mu yi dodon bango ba.