Zaɓe: Gwamnatin Tarayya ta rufe jami’o’i na makonni 3

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ta bai jami’o’in Nijeriya umarni kan su rufe daga ranar 22 ga Fabrairu zuwa 14 ga Maris saboda zaɓuɓɓukan da za a gudanar ran 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris, 2023.

Gwamnati ta ba da umarnin ne domin bai wa ɗalibai, malamai da saunran ma’aikata a jami’o’i damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓukan.

Umarnin na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Fabrairu wadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta aike wa jami’o’i a faɗin ƙasa.

Cikin sanarwar mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Sakataren NUC, Dakta Chris Maiyaki, hukumar ta ce kare ma’aikata da daalibai da kadarorin gwamnati na daga cikin dalilan da suka sanya ɗaukar wannan mataki.

“Duba da yadda lamurra ke tafiya da kuma damuwa da batun tsaron ma’aikata da ɗalibai da kadarorin gwamnati a jami’o’i, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bai wa ɗaukacin jami’o’i umarni da cibiyo masu alaƙa da su kan su rufe daga 22 ga Fabrairu zuwa 14 ga Maris, 2023,” in ji sanarwar.

NUC ta ce kafin ɗaukar wannan mataki sai da Ministan ya nemi shawarwari daga hukumomin tsaron da lamarin ya shafa.