Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Naja’atu Bala Mohammed

Daga FATUHU MUSTAFA

Zuwa ga Gwaggo Naja’atu Bala Mohammed:

Bayan dubun gaisuwa da fatan alheri, na saurari wata hira da kika yi, wacce ita ce ta farko, tun bayan da kika fice daga cikin tawagar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. A cikin wannan hira, kin bayyana cewa, kin fice ne, sakamakon fahimtar da kika yi na cewa, Asiwaju ba ya da wani tanadi da ya yi wa Arewa. A kan wannan nake da ja! Domin dai ni ganau ne ba jiyau ba.

Domin a magana ta gaskiya, in har aka ce Asiwaju baya da wani tanadi da ya yi wa Arewa, kuma ina wurin na yi shiru, to a gaskiya ban yi wa kai na adalci ba, domin kuwa ni ganau ne ba jiyau ba. Kusan zan iya cewa, ya taka rawa a duk wani kundi ko ƙasida da ya yi a Arewacin ƙasar nan, ɗari bisa ɗari. Tun daga shekarar da ta gabata zuwa yau ɗin nan.

A haƙiƙanin gaskiya, kamar yadda Malam Abdulaziz Abdulaziz ya bayyana, ya gabatar da ƙasida a zauren taro na Arewa House, ya kuma bayyana ayyukan da yake fatan ya yi wa Arewa, ciki kuwa har da batun tashar jirgin ruwa ta Baro, wutar Mambila, aikin dogo daga Kano zuwa Legas, aikin dogo na Kano zuwa Maraɗi, yaƙi tuƙuru da ‘yan ta’adda da suka addabi al’ummomin Arewacin ƙasar nan, da wasu da dama.

A taron da ya yi da manoma a Birnin Minna na Jihar Neja, Asiwaju ya bayyana irin tsarin da ya yi wa noma a Arewa, dama wasu sassa na ƙasar nan, wanda kowa ya san ginishiƙin tattalin arzikin Arewa noma ne. Cikin abubuwan da yake fatan idan Allah ya biya masa buqata ya yi, sun haɗa da:

Havaka gandun daji a duk faɗin Arewacin ƙasar, saboda ya samarwa da makiyaya wuraren kiwo masu yalwa da kuma aminci, ya daƙile kwararowar hamada, wacce ke kashe mana gonaki da kuma qaranta wuraren kiwo. Samar da tallafin kuɗi da kayan aiki ga manoma musamman masu noman hatsi, domin a samu wadatar abinci a ƙasar nan.

Samar da tsaro a dazuzzukanmu domin manoma su samu su yi noma a cikin kwanciyar hankali. Samar da kasuwar manoma ta duniya, inda manomi zai iya tallata kayansa ga masu saye a duk inda suke a faɗin duniya. Waɗannan, da ma wasu da dama na qunshe cikin ƙasidarsa da ya gabatar a Minna a yayin taron tattaunawa da ya yi da ƙungiyoyin manoma na Arewa a Minna, ran 7 ga watan Nuwamba 22.

Mu komo batun Kano, a ranar 22 ga Oktoba na 2022, Asiwaju ya yi zama na musamman da ‘yan kasuwar Kano a Gidan Gwamnatin Kano, a yayin wannan tattaunawa, ya bayyana tanadin da ya yi wa, harkokin noma, masana’antu da kasuwanci a Kano.

Kaɗan daga cikin irin waɗannan tanade-tanade sun haɗa da yashe madatsun ruwa guda 19 da Kano take da su, da kuma inganta su saboda haɓaka noman rani, da kuma taqaita yawan ambaliyar ruwa da ake samu lokacin damina. Sake fasalin filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, farfaɗo da rukunin masana’antu na Kano da ke Sharada, Bompai, Challawa, Tokarawa da Jogana.

Gyara fasalin kasuwar Dawanau domin ta zama cibiyar hada-hadar kasuwancin noma ta ƙasashen duniya, ƙarasa aikin samar da bututun gas da ya taso daga Lakwaja zuwa Kaduna zuwa Kano.

Ina ganin ko a nan aka tsaya, to akwai tabbacin Asiwaju ya yi wa Arewa, tanadin da a duk cikin ‘yan takarkarunmu ba wanda ya yi mata. Ta ya kuma za a ce, ba shi da wani tanadi da ya yi wa Arewa?! Ƙila kuma ni ne ban fahimci abin ba.

Sai dai abin tambaya a nan shi ne, shin shi Atiku wanne tanadi ya yi wa Arewa? Ina ga wannan ne abinda ya kamata a tambaya, idan akwai sai ya kawo, sai mu haɗa biyun mu ga wanne ne zai fi amfanar Arewa, tsakanin tanadin Asiwaju da na Atiku! Allah ya bamu sa’a!

Fatuhu mustafa, Marubuci ne, kuma ɗan ƙasa mai saharho a kan al’amuran ƙasar nan. Ya rubuto daga Abuja