Ba sai kana da jari ne za ka iya yin sana’a ba – Binta Tukur Nadada

“Sha’awa ta ga ƙirƙira ce ta sa ni yin sana’ar ƙera gadaje”

Daga ABUBAKAR M. TAHIR

Hajiya Binta Tukur Nadada ‘yar asalin garin Bakori ce da ke Jihar katsina. Yar boko ce kuma mai sha’awar ƙirƙire-ƙirƙire, inda yanzu haka ta ke sana’ar ƙera kayan ɗaki irin su gado, kujeru da makamantan su. Hajiya Binta ta fito ne daga tsatson marigayi Makaman Katsina na Uku. Kuma a halin yanzu tana digirinta na uku kan yadda za a tallafa wa mutane su kafa kasuwancinsu don tsayawa da koafafunsu, wadda ta tabbatar ya fi raja’a ne ga matan Arewa. Yanzu haka Hajiya Binta ita ce mamallakiyar kamfanin nan na ƙera kayan ɗaki, mai suna Bahazcraft. A tattaunawarta da wakilin Manhaja, ta kawo dalilan da ya sa ta ke son zama mace da ta dogara da kanta da kuma irin faɗi-tashin da ta yi a harkar kasuwancinta. Don haka, mai karatu, a sha karatu lafiya.

MANHAJA: Da farko mai karatu zai so ya ji wacce ce Binta Tukur.

HAJIYA BINTA: Assalamu alaikum warahamatullah. Da farko sunana Hajiya Binta Tukur Nadada. Haifaffiyar garin Bakori da ke Jihar Katsina. Kuma ni jinin sarauta ce, domin kasancewata jinin Makaman Katsina na Uku, marigayi Makama Tukur.

Na yi karatun firamare da sakandare duk a cikin garin Bakori, daga bisani na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, na karanci lissafi, wato B.sc Accounting. Kuma Allah cikin ikonSa na kammala a shekara ta 1997 da sakamako mai kyau.

Kasancewar Ina da matuƙar son karatu ya sa ban yi ƙasa da gwiwa ba, na koma jami’ar dai ta Zariya, na yi digiri na biyu a ‘Finance and Accounting’, inda na kammala a shekarar 2003. Ban haƙura ba, na sake komawa na sake yin wani digirin na biyu a ɓangaren kasuwanci da ƙirƙire-ƙirƙire, wato ‘Business Administration, Innovation and Marketing’.

Yanzu haka Ina kan digiri na uku a ɓangaren yadda za a tallafa wa mutane su kafa kasuwanci, musamman Arewacin Nijeriya. Ina da aure, kuma Allah Ya albarkace ni da samun ‘ya’ya uku. Alhamdu lillah.

Yaushe ki ka fara kasuwanci musamman irin wannan na ƙirƙirar wasu abubuwa?

To, alhamdu lillah. Gaskiya tun tasowa ta ba ni da sha’awar ace Ina ƙasan wasu, Ina mu su aiki koda kuwa gwamnati ce, wannan tasa tun Ina ƙarama Ina da sha’awar ƙirƙire-ƙirƙire tun lokacin Ina firamare na kan ciro ganyen zoɓo a lambun gidanmu, na daka shi, Ina tunanin cewa, za a iya maida shi ganyen shayi tunda a da ana amfani da shi ne wajen kwaɗon rama.

Da ire-iren waɗannan tunanin har na kai ga tunanin yadda san samar da gun sarrafa kayan gado, duba da irin yadda muke kashe maƙudan kuɗaɗe wurin shigo da su daga wasu ƙasashen. A iya tunanina duk wani abu da ake buqata na sarrafawa su zama gado ko kujeru tun daga shi kansa katakon zuwa sauran kayan haɗi, Allah Ya azurta ƙasarmu da su.

To, da wannan tunani na fara da gyara kayan ɗaki na gidana, da kaina na yi. Daga nan da wata mata gani, ta tambaye ni wanda ya yi min, na sanar da ita ai ni da kaina na yi. Shine fa ta nuna sha’awarta har ta buqaci in yi mata irin su, ta ba ni dubu goma kafin alƙalami, na fara aiki.

Bayan an yi mata, ta fara sanar da mutanen da ke tambayar ta ai ni ce na yi mata, to daga nan ne aka fara sanin Ina wannan sana’a, kuma mutane suka fara kawo aikin su. Da abin ya fara bunƙasa, sai maigidana ya buɗe min shago, na fara aikin a can.

A shekarar 2009 ne ya zama kamfani mai zaman kansa, wanda aka sanya wa suna BahazCraft, inda na yi amfani da sunaye masu muhimmanci a rayuwata a sunan.

A haka sai ya zama muna samar da kayan gado, kujeru da lokoki, amma na zamani, waɗanda muke inganta su tare kuma da tafiya da zamani.

Haka kuma ta ɓangaren kayan da ke fita marar amfani, kamar guntuwar katifa ko guntun katako, muna sarrafa shi don fitar da wani abu da za a yi amfani da shi, ma’ana dai muna tabbatar da amfanuwar kusan komai. Alhamdu lillah, muna ganin cigaba a kowane lokaci, ba abin da za mu cewa ubangiji sai godiya.

Da yake kasuwanci na buƙatar tanaji, shiri da ma sanin ilimin sa. Shin daga fara sanarki ne ki ka fara tunanin komawa makaranta domin karanta ilimin kasuwanci gadan-gadan?

Bayan kammala digiri ɗina kamar yadda na fada maka na fara tunanin buɗe kamfani inda tun Ina ƙarama da yake Ina son ace Ina ƙirƙira wannan tasa na koma makaranta domin ci gaba da karantar kasuwanci a zamanance da ma hanyoyin da za a ingantashi.

Ta ɓangare ɗaya, kasuwamci na buƙatar tanadi kamar yadda ka faɗa, abin nufi, ka san abinda ka ke son yi, wato ya zamana sana’ar duk da za ka zaɓa ya zamana zuciyarka ta aminta da ita, ma’ana ka yi sana’ar da ka ke so, ba wadda kaga wasu na yi ba, hakan zai sa ka saka hankalinka sosai da kuma lokacin ka wurin yin sana’ar. Wannan shi ne shirin da ka ke buƙata a sana’a ba dole sai da jari ba, saboda za ka ma iya rancen kuɗi ka fara. Kamar ni kaga da ‘deposit’ na fara na ‘customer’ har ya zama na zama mai kamfani.

Idan ka yi duba da irin arzikin da Allah Ya yi mana a ƙasar nan, na daga yawan adadin mutane da muke da su da suka kai miliyan ɗari biyu, sannan Ya bamu albarkatu masu yawa, ta yadda kusan duk wani abu da ka ke nema na sarrafawa akwai shi a Nijeriya. Idan ka ɗauki vangare na, tun daga katako zuwa katifa ba wanda ba a wadata mu da abin sarrafa su ba.

Abin da kawai muke buƙata shine inganta ababen da muke yi, wanda hakan na hannunmu ne, kuma abu ne da zai kai mu ga nasara. Duk abinda za ka yi, ka inganta shi, ya zama ‘standard’ domin shi kasuwanci yana buƙatar mai shi ya san irin buƙatar mai siya. Baya ga haka, kada ya zama neman kuɗin ne ya rufe ma ka ido kawai, ma’ana riqe gaskiya ta zama jagaba a tafiyar kasuwancinka, ya zama duk wanda ya yi hulɗa da kai yana sha’awar dawowa don kyakyawar mu’amala da ya yi da kai, wannan zai sa ka samarwa kanka ɗan tallan kasuwancin naka, domim ta hakan ne zai sa wanda ka yi mu’amala da shi ya dinga turoma wasu don yana da tabbaci kanka.

Idan muka yi duba da rayuwa gabaɗayan ta cike ta ke ƙalubale, kuma kasuwanci na ɗaya daga cikin ababen da ke tattare da ƙalubale na faɗi tashi. Shin waɗanne irin matsaloli ki ka fuskanta a kasuwancin naki da ma rayuwar bakiɗaya?

Da wannan tambayar za mu dasa aya, wadda muke fatan a sati mai zuwa baƙuwar tamu zata fara da ba mu amsar ta kafin wasu tambayoyi da za su biyo baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *