Dubun masu tiransifa ta ƙarya ta cika a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a KANO

Rundunar ‘yan sandan jiyhar Kano ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da damfarar wani mai shago a Sharaɗa da ke Ƙaramar Hukumar Binni ta jihar.

Rahotanni sun nuna an kama waɗanda ake zargin, Mujihid Kabir da Abdu Imam da laifin damfara, sata da kuma kutse.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kama su a ranar Talatar da ta gabata,

Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa a ranar 2 ga watan Fabrairu daga Sharaɗa cewa wasu mutum biyu sun sayi shinkafa a wani shago inda suka tura kuɗi ta hanyar tiransifa ta bogi, wato ‘Fake Alert’, sannan suka yi awon gaba da shinkafa buhu ɗaya.

“Bayan samun wannan kiran gaggawa Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Mamman Dauda, ya tura jami’an ‘yan sanda zuwa wannan wuri ƙarƙashin jagoranci DPO na Sharaɗa SP Abdulrasheed Adamu, inda ya ba su umarnin lalle a tabbatar an kamo waɗanda suka aika wanann mummunan aiki.

Kiyawa ya kiara da cewa, ba tare da ɓata lokaci ba aka kama wasu mutane biyu da ake zargi da suka haɗar da Mujahid mai shekaru 30 da ke Ahmadu Bello Way, sai kuma abokinsa Abdu dan kimanin shekaru 30 da ke Unguwar Zoo Road duk a jihar Kano.

“Binciken farko ya nuna waɗanda ake zargin sun tabbatar da cewa sun je shagon ne domin su damfari mai shagon inda suka sayi kayan sa kuma suka tura masa kuɗin, wato tiransifa ta bogi domin arcewa da wannan shinkafa.

Ya ce bayan zurfafa bincike ne aka gano katin shaidar aikin arida (ID Card) na gidan Radiyon Vision a wurin masu laifin, inda ya bayyana cewa hakan tasa suka garzaya zuwa gidan Rediyon Vision don jin ko ma’aikatansu ne.

Sai dai kuma hukumar gudanarwar gidan Radiyon Vision ta bayyana cewa sun taɓa ganin waɗannan mutane sau ɗaya inda a wannan zuwa ne suka sace katin shaidar aikin Jarida na wani ma’aikacin gidan kuma suka je suka buga na bogi domin yin sojan gona da shi.

A zantawar manema labarai da Mujahid Kabir, ya ce:

“Sun je shagon mai sayar da kayayyakin ne domin yin sojan gona da katin shaidar aikin Jarida na gidan Radiyon Vision, inda suka sayi shinkafa kuma suka tura kuɗi ta hayar tiransifa ta bogi wanda rashin ganin kuɗin ya sa mai shagon ya kira jami’an tsaro don kawo musu ɗauki.”

Ya ƙara da cewa yadda aka yi suka sami wannan katin shaidar aikin Jarida, “sun je gidan Rediyon Vision ne domin a yi musu talla a nan ne suka sami damar sace wanann ‘ID Card’.

Sun ce sha’awar aikin Jarida ne yasa suka sace wannan ID Card inda kuma ya ce wannan shi ne karon farko da suka aikata irin wannan damfara.

Kakakin ‘yan sandan ya ce yanzu haka Kwamishinan ‘yan sanda ya bada umarnin a turasu zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da gudanar da bincike.

“Da zarar mun Kammala bincike na manyan laifuka da suka aikata na haɗin baki, sata, damfara da kuma kutse za a gurfanar da su a gaban kuliya dan gane shayi ruwa ne,” in ji SP Abdullahi Kiyawa