Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
‘Yan Nijeriya na cigaba da fuskantar sauye sauye a ɓangaren siyasa, tattalin arziki da zamantakewa da aka jima ba a gani ba a ƙasar nan. Kusan hankalin kowa a farke yake, cikin tunanin me yake faruwa?
Me zai faru? Wanne tasiri hakan zai yi a rayuwar mu? Ko ban yi bayani ba, na san wasu sun fara gano bakin zaren maganar da nake son nazarinta a wannan makon.
Tun shigowar gwamnati mai ci ta shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ƙarƙashin Jam’iyyar APC a shekarar 2015, ‘yan Nijeriya sun ga tsare tsare iri iri da gwamnati ta ɗauka da manufar inganta ƙasa a ƙoƙarin ta na cika alƙawuran da ta yi wa ‘yan ƙasa a lokacin yaƙin neman zaɓe, waɗanda suka shafi bunƙasa tattalin arziki, yaƙi da cin hanci da rashawa, da kuma yaƙi da ta’addanci.
Duk da ƙalubalen da rayuwar ‘yan Nijeriya ta fuskanta na ƙunci da tsadar rayuwa a ƙarƙashin wannan gwamnati, ba za a ce gwamnati ba ta yi rawar gani a wasu ɓangarorin na raya ƙasa da tallafa wa walwalar ‘yan Nijeriya ba. Musamman a vangaren ba da tallafin kuɗaɗe ga matasa da masu ƙananan sana’o’i, samar da tallafin rage basussukan albashi ga wasu jihohin ƙasar nan, farfaɗo da ayyukan noma, ƙarfafa rundunar tsaron Nijeriya, inganta rayuwar masu fansho, da bankaɗo badaƙalar kuɗaɗe da wasu suka yi rub da ciki a kai, da tono badaƙalar satar ɗanyen man fetur. Tabbatar da gano ɗanyen man fetur da iskar gas a arewacin ƙasar nan, da gyaran wasu manyan hanyoyin ƙasar nan.
Ko da yake ba za a ce an samu nasarar da ake nema ba, saboda ayyukan ‘yan ta’adda na cigaba da gudana a wasu sassan Nijeriya, tsadar abinci da rashin kuɗi a hannun mutane na cigaba da gasa mutane. Ƙalubalen masu garkuwa da mutane da ‘yan makaranta na nan ana fuskanta. Wasu abubuwan da tsare-tsaren gwamnati suka haifar a rayuwar talakawan ƙasar nan, ya sa ba kasafai ‘yan ƙasa ke tunawa da waɗancan nasarori da ayyukan alheri da gwamnati ta samar ba, saboda kuwa ba sa gani a ƙwaryar tuwonsu.
Tsare-tsaren gwamnati na rufe iyakokin ƙasar nan, don hana shigo da wasu muhimman kayayyaki da suka haɗa da kayan abinci, da nufin bunƙasa noman shinkafa da ƙarfafa gwiwar ‘yan Nijeriya su riƙa ciyar da kansu ta hanyar noma da kiwo. Duk da tallafin da aka ce an bai wa wasu manoma da nufin samun ƙarfin jarin yin noma ƙananan manoma ba su gani a ƙasa ba, domin sun yi zargin wasu masu uwa a gindin murhu ne aka bai wa.
Wannan tsari na rufe iyakoki ya haifar da tsadar abinci da tashin farashin kayan masarufi a Nijeriya, saboda tsadar da mudun shinkafa ya yi, kafin shinkafar gida ta fara fita da farashi mai sauki.
Jama’a sun wahala sosai kuma hakan ya jawo wa gwamnati tofin Allah tsine, tare da zargin ta da rashin tausayin talakawa. Duk kuwa da shawarwarin masana tattalin arziki na buƙatar sassauta wannan doka, don ‘yan ƙasa su samu sauƙi.
Amma gwamnati ta yi ko gezau da waɗannan shawarwari. Daga baya dai manoman shinkafa sun dara, kamfanonin casar shinkafa da gyara ta sun yawaita, amma duk da haka farashin kayan abinci na daɗa hauhawa. Abinci ya wadata a qasa, amma kuɗin saye ya yi wuya a hannun talaka.
Kwatsam sai ga batun canjin kuɗi ya taso, inda Babban Bankin Nijeriya na CBN ya sanar da canza launin manyan kuɗaɗen Nijeriya da suka haɗa da Naira dubu ɗaya, 500, da 200, da ƙara inganta tsaronsu da aka yi. Wannan kyakkyawar manufa ta gwamnatin tarayya ta zo wa ‘yan Nijeriya a matsayin bazata, ta kuma sauya musu salon rayuwa.
Kamar yadda jami’an Babban Bankin Nijeriya suka bayyana canjin kuɗin na da muhimmanci, domin daile ayyukan ‘yan ta’adda, da masu karvar kuɗin fansa, da masu sayen ƙuri’a a lokacin zave, da masu tara kuɗi a gida ba tare da amfani da shi ba, alhalin talakawa na rayuwa cikin rashin kuɗi da tsadar rayuwa. Sannan da kuma rage yawan amfani da tsabar kuɗi a hannun jama’a, da wuraren kasuwancin su.
Za a iya cewa, burin gwamnati ya cika, an ga yadda aka riƙa fitar da tsofaffin kuɗin da aka taskace su a gidajen masu kuɗi da manyan ‘yan kasuwa, ana ta fito da su zuwa bankuna, duk kuwa da ƙarancin lokacin da aka bayar a baya na watanni uku kacal, kafin daga bisani a ƙara wa’adin. Wannan shi ma ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali, saboda ba a samu wadatar sabbin kuɗaɗen ba, kuma wa’adin cigaba da musanyen tsofaffin yana ƙurewa.
Hada-hadar kasuwanci ta tsaya cak, saboda kowa na gudun asara. Cinikayya ta koma ta na’urar aikawa da kuɗi na bankuna ko na masu shaguna ta POS. Tsabar manyan kuɗi a hannu ta gagara ganuwa.
Masu cefane ba su da asusun ajiya na banki, masu cire kuxi ta POS kuma sun tsawwala farashin da suke karva wajen cire kuxi. Kowacce Naira dubu 10 idan za ka cire sai sun karvi dubu 1, a irin wannan yanayin su ma masu POS ɗin dole kasuwar su ta kwanta kowa ya gudu.
Babu ƙananan canji, cinikayya ta gida da gida a tsakanin mata ita ma ta shiga tasgaro. Masu ƙananan kasuwanci sun daina ciniki, komai ya rikice. Babu ma mai tunanin bayar da sadaka ko taimakon kuɗi, mutane sun rasa alƙiblar da suka dosa.
Wasu rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta sun bayyana cewa, an ga wasu ‘yan ta’adda suna rarraba wa matafiya tsofaffin kuɗin Naira a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno da ke Jihar Borno! Aƙalla kowane matafiyi yasa mu Naira N100,000 daga hannun waɗannan yan ta’addan daji a hanyar jihar Barno!
Shin ko hakan ya tabbatar da alfanun sauya fasalin kuɗaɗen da CBN ke zargin wasu na riqe da kuɗin haram a ƙasar nan?
Talakawan Nijeriya sun harzuƙa sosai da halin da suka samu kansu a ciki, daf da lokacin da ake shirye-shiryen sallamar gwamnatin Baba Mai Gaskiya, wanda suka nunawa tsananin ƙauna da soyayya, suka yi wa fatan ganin ya gyara ƙasar nan fiye da yadda ya same ta.
Sai ga shi tunanin su da burinsu ya juya ya zama mafarki, sun samu kansu cikin matsanciyar rayuwa da talauci. Yayin da su kuma a nasu vangaren hankalin ‘yan siyasa ya karkata wajen yaƙin neman zaɓe.
A ƙarshen makon da ya gabata ne, wasu fusatattun matasa a birnin Kano suka jefi ayarin motocin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da jirgin saman da aka ce yana ciki, domin bayyana vacin ransu ga halin ƙuncin da gwamnatinsa ta jefa rayuwar talakawa a ciki.
Duba da yadda harkokin kasuwanci suka tsaya cak a birnin na Kano, da yake zaman cibiyar kasuwanci ta Arewa da na yankin Afirka ta Yamma. Wannan abu ne da ya zo wa mutane a bazata, ganin irin ɗimbin masoya da goyon bayan da shugaba Buhari yake da shi a Kano, amma talakawa sun masa bore, don nuna qin jinin su da manufofin gwamnatinsa da suke quntatawa rayuwar ‘yan ƙasa, duk da yake masana na ganin hakan yana da alfanu ga cigaban tattalin arzikin ƙasar nan.
Ya kamata hukumomi da masu faɗa a ji su riqa la’akari da talakawa da halin da rayuwarsu za ta shiga, sakamakon irin tsare tsaren su da ƙudirorinsu na cigaba, a riƙa sauraron koke-kokensu, ana kuma faɗakar da su yadda ya kamata, don bai wa gwamnati haxin kai da goyon baya, a duk lokacin da ta fito da wani tsari, don cigaban ƙasa da inganta rayuwar al’umma.
Muna sane da cewa, manufofin gwamnati masu kyau ne, kuma ba a fitar da su don ƙuntatawa jama’a ba, sai dai idan an samu akasi ba hujja ba ce talakawa su ɗauki doka a hannu ba, domin gudun illar da hakan za ta haifar ga zaman lafiya da zamantakewar al’umma.
