Tinubu ya ƙaddamar da shirin bai wa matasa rancen mallakar kwamfutoci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Lamunin Jari da ƙarfafa Kasuwanci (CREDICORP) ta ƙaddamar da sabon shirin bayar da rancen kayan aikin zamani domin bai wa matasan Nijeriya damar mallakar kwamfutocin tafi-da-gidanka da sauran na’urorin fasaha cikin sauƙi.

An ƙaddamar da shirin ne, mai suna Credit for Laptops, Internet, Connectivity and Knowledge Digital Devices (C.L.I.C.K.D.), a Abuja, tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Fasahar Zamani ta Tarayya.

A cewar CREDICORP, shirin zai fara ne da samar da kwamfutoci 1,000 da aka haɗa a cikin Nijeriya ga waɗanda suka cancanta a ƙarƙashin shirin horas da ƙwararrun matasa miliyan uku na Gwamnatin Tarayya (3MTT), inda mutum 77 suka karɓi kwamfutocinsu a wajen bikin ƙaddamar da shirin.

Hukumar ta bayyana cewa bankin Fidelity ne zai kula da gudanar da tsarin lamunin, yayin da Hukumar Kula da Kimiyya da Kayayyakin Injiniya ta ƙasa (NASENI) tare da Imose Technologies za su riƙa haɗa kwamfutocin a cikin ƙasar.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Ministan Sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Dijital, Bosun Tijani, ya ce manufar shirin ita ce tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ba wai sun samu horon fasahar zamani kaɗai ba, har ma suna da kayan aikin da za su ba su damar cin gajiyar tattalin arzikin dijital.

Ya ce, tattalin arzikin dijital ba zai bunƙasa yadda ya kamata ba sai idan matasa sun samu ilimi tare da kayan aikin da za su yi amfani da su.

Ministan ya ƙara da cewa shirin C.L.I.C.K.D. zai taimaka wa waɗanda suka cancanta a cikin shirin 3MTT su shiga duniyar fasahar zamani cikin sauƙi, tare da ƙarfafa masana’antun cikin gida ta hanyar amfani da kwamfutocin da aka haɗa a Nijeriya.

Shi ma Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya bayyana cewa sabon tsarin zai kawar da babban ƙalubalen kuɗin sayen kayan aikin dijital, tare da bunƙasa tsarin lamunin mabukaci cikin tsari da kuma tallafa wa masana’antun cikin gida.

A cewarsa, shirin zai mayar da kayan aikin dijital daga abin da ke hana ci gaba zuwa wata dama ga matasa, domin zai ba su hanyar samun kayan aikin da suke buƙata domin koyo, aiki da samun kuɗin shiga ba tare da wahalar biyan kuɗi gaba ɗaya lokaci guda ba.

Ya ce hakan kuma zai taimaka wajen cimma manufar gwamnatin tarayya ta bunƙasa masana’antu da samar da ayyukan yi.

CREDICORP ta bayyana cewa C.L.I.C.K.D. shi ne babban shirin da ta tanada na ba da rancen kayan aikin fasaha, kuma daga baya za a faɗaɗa shi zuwa sauran na’urorin da ke amfani da intanet da kuma kayan aikin dijital ga ma’aikata da sauran ‘yan Nijeriya.

Kamfanin ya kuma ce yana shirin haɗa hannu da ƙarin cibiyoyin kuɗi, masana’antun na’urori, kamfanonin fasaha, Babban Bankin Nijeriya (CBN), cibiyoyin horaswa da sauran abokan hulɗa domin faɗaɗa damar samun kayan aikin dijital masu araha a faɗin ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply