Tinubu ya jaddada ƙarfafa dangantakar Nijeriya da Birtaniya a fadar Sarkin Ingila

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada muhimmancin dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da ƙasar Birtaniya, inda ya bayyana ta a matsayin alaƙa mai zurfin tarihi, haɗin kai da kuma hangen makomar gobe.

Yayin da yake jawabi a liyafar ƙasa da Sarki Charles III ya shirya a Fadar Windsor ranar 18 ga Maris, 2026, Tinubu ya ce babban abin alfahari ne gare shi ya wakilci Nijeriya a wannan wuri mai cike da tarihi, yana mai cewa taron na nuna irin ƙaƙƙarfan alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaban ƙasar, wanda ke ziyarar aiki a Birtaniya, ya nuna godiya ga sarkin da mai ɗakinsa Sarauniya Camilla bisa kyakkyawar tarbar da aka yi masa, matarsa da tawagarsa.

Ya kuma bayyana jawabin nasa a matsayin tarihi, kasancewar shi ne na farko da wani shugaban Nijeriya ya gabatar a Fadar Windsor.

Tinubu ya yi bayani kan yadda tsarin siyasa da na shari’a na Birtaniya suka yi tasiri a Nijeriya, inda ya ambaci tarihin Magna Carta da kuma gudunmawar masana falsafa irin su John Locke da Thomas Hobbes.

Ya ce, tsarin shari’a, majalisar dokoki da ma’aikatar gwamnati a Nijeriya sun samu tasiri daga waɗannan ginshiƙai.

Haka kuma, ya jaddada alaƙar al’adu da harshe tsakanin ƙasashen biyu, inda ya yi nuni da tasirin harshen Turanci a duniya da kuma fitattun marubuta irin su William Shakespeare da Charles Dickens.

Dangane da alaƙar jama’a, shugaban ya yaba wa ‘yan Nijeriya mazauna Birtaniya, musamman gudunmawar da suke bayarwa a National Health Serɓice da sauran fannoni. Ya kuma ambaci fitattun ‘yan wasa ‘yan asalin Nijeriya da ke wakiltar Birtaniya irin su Bukayo Saka, Eberechi Eze da Anthony Joshua a matsayin alamar haɗin kan jama’a tsakanin ƙasashen biyu.

Tinubu ya kuma bayyana cewa Nijeriya da Birtaniya na ci gaba da aiki tare a ƙarƙashin Commonwealth of Nations, yana mai jaddada aniyar Nijeriya na ƙarfafa rawar da ƙungiyar ke takawa a ci gaban duniya.

A fannin tsaro, shugaban ya amince da ƙalubalen ta’addanci da ke addabar yankin Yammacin Afirka, musamman yankin Sahel, yana mai cewa haɗin gwiwa da Birtaniya na da matuƙar muhimmanci. Ya kuma bayyana shirinsa na ganawa da Keir Starmer domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban.

Yayin da yake waiwaye kan tafiyar dimokuraɗiyyar Nijeriya, Tinubu ya gode wa Birtaniya bisa goyon bayan da ta bayar a lokacin mulkin soja, inda ya tuna da rayuwarsa ta gudun hijira a wancan lokaci, yana mai cewa wannan goyon baya na da matuƙar muhimmanci a tarihin ƙasar.

A ƙarshe, shugaban ya bayyana kyakkyawan fata game da makomar dangantakar Nijeriya da Birtaniya, tare da gayyatar mahalarta taron su ɗaga kofin murna domin ci gaba da ƙawance tsakanin ƙasashen biyu.

Ya ce, “Tare, za mu gina makoma mai haske bisa girmamawa juna, haɗin gwiwa da kuma makoma guda.”

By ukarofi