Tinubu ya karrama sosjojin da aka kashe da lambar MON

*Ya ɗauki nauyin karatun ‘ya’yansu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karrama sojoji 17 da aka kashe kwanan nan a Jihar Delta da lambar yabo ta ƙasa (MON).

Huɗu daga cikin marigayan aka karrama da lambar MON, yayin da sauran 13 suka samu lambar ‘Officers of the Federal Republic’.

Haka nan, Tinubu ya sanar da ɗaukar nauyin karatun ‘ya’yan marigayan da kuma kyautar muhalli ga iyalansu.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin jana’izar marigayan wadda aka gudanar a ma koabartar sojoji da ke Abuja.

Sojojin sun cimma ajali ne ranar 14 ga Maris a hannu ɓata-garin yankunan Okuama da Okoloba a lokacin da suka tafi aikin tabbatar da zaman lafiya.