Gwamna Lawal ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hanzarta kammala ayyukan madatsun ruwa a Zamfara

Daga BASHIR ISAH

A matsayin ɓangare na ƙoƙarin da Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ke don wadata jiharsa da tsaftataccen ruwan sha, hakan ya sa Gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta kammala ayyukan madatsin ruwa da ke gudana a jihar.

Lawal ya yi wannan kira ne a ranar Talata sa’ilin da ya ziyarci Ministan Albarkatun Ruwa, Injiniya Fatgesa Joseph Terlumun Utsav.

Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, tattaunawa jagororin ta ta’allaƙa ne kan ayyukan samar da ruwan sha a Zamfara.

Suleiman ya ce yayin tattaunawar tasu, Gwamna Lawal ya yi bayani kan muhimmanci madatsun ruwa wajen samar wadataccennruwan sha ga jihar wadda ke fuskantar ƙaruwar jama’a domin bunƙasa harkokin noma da tattalin arziki.

Lawal ya jaddada buƙatar da ke akwai Gwamnatin Tarayya ta ware isassun kuɗaɗe domin kammala ayyukan madatsun ruwan da ke gudana a jihar saboda muhimmancinsu ga cigabana al’umma.

A nasa ɓangaren, Ministan ya yi wa Lawal alƙawarin ma’aikatarsa za ta tura tawagar ƙwararru zuwa Zamfara nan ba da daɗewa ba domin duba yanayin ruwa a jihar don bada shawarwarin da suka dace.