Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dokta Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi da ya ci gaba da haɗa kai da magabacinsa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, domin samun haɗin kan jam’iyyar da kwanciyar hankali.
Manhaja ta ruwaito cewa Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin da Ganduje ya kai masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa.
Ya jaddada cewa duk da ya gaji Ganduje, jagorar tsohon shugaban da gogewar siyasa za su yi matuƙar amfani wajen samun nasarar mulkinsa.
“Maigirma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya roƙe ni da in yi aiki tare da ku, don tuntuɓar ku har ma game da haɗin gwiwa, na ce masa har yanzu zan ɗauke ku a matsayin shugaba tare da haɗin gwiwa da ni. Har yanzu kai ne shugaban jam’iyyar,” inji Yilwatda.
Ganduje, wanda ya riƙe muƙamin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa bayan ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Kano, ya yi murabus ne a ranar 27 ga watan Yuni bisa wasu lamurra da suka taso.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa zuwa ga sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Ajibola Bashiru, ya bayyana rashin lafiya a matsayin dalilinsa na murabus.
Ficewar tasa ta share fagen nada Yilwatda a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC a ranar 24 ga watan Yuli.
A yayin ziyarar, Yilwatda ya yi watsi da matsayinsa na cikakken shugaban jam’iyya mai mulki, yana mai bayyana kansa a matsayin “kodineta” da ke da alhakin haɗa kan ‘yan jam’iyya.
Ya ba da labarin abubuwan da ya fara tunowa a siyasance, inda ya banbanta tarihin Ganduje na tsawon shekaru da dama da nasa na kwanan nan.
“Jam’iyyar ta mu ce, dukkanmu shugabannin jam’iyyar ne na gama-gari, sannan kuma bisa gogewa da sanin makamar siyasa kun kasance a can gabana, tun zamanin NPN kuna cikin fagen siyasa.
A lokacin ina makarantar firamare ne kawai. Na tuna ganin Gwamna Rimi ya ziyarci Solomon Lar a Jos a karshen shekarun 70 zuwa farkon 80s. Ina nan a Form 2, ina ta hannu da abokan karatuna, ban san ainihin ma’anar siyasa ba, alhali ka riga ka mallaki igiya,” ya shaida wa Ganduje.
Ya ƙara da cewa zai dogara kacokan ga “Kwarewa, abokan hulɗa, da alaƙar Ganduje” don tabbatar da matsayin APC a faɗin ƙasar nan da kuma tabbatar da nasarar zaɓe a nan gaba.
A nasa jawabin, Ganduje ya bayyana jin daɗinsa da kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da magajinsa, inda ya bayyana cewa rikici tsakanin magabata da waɗanda suka gaje shi ya daɗe yana addabar siyasar Nijeriya.
“Abu mai mahimmanci shi ne matsalar da ke tsakanin magaji da wanda ya gabace shi na daya daga cikin abubuwan da APC ta warware.
Tun daga shekarar 1999, matsalar da ke tsakanin tsofaffin gwamnoni da waɗanda suka gaje su ta kasance matsala ce a yawancin jihohin tarayyar ƙasar nan. Ba wai kawai a gwamna ba, har ma a wasu muƙamai.
“Don haka dangantakarmu ita ce farkon magance irin wannan matsala, ba wai a APC kaɗai ba, har ma a dukkan yanayin dimokuraɗiyya,” inji Ganduje.
Ya taya Yilwatda murnar naɗin da aka yi masa, ya kuma yi alƙawarin bayar da goyon bayansa wajen gina jam’iyyar APC mai ƙarfi.
