Tinubu zai fara biyan manyan jami’an tsaron cikin gida har ƙarshen rayuwarsu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Harkokin Cikin Guda, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, a jiya Alhamis, ya sanar da wata muhimmiyar manufa ta jin daɗin jama’a da Shugaba Bola Tinubu ya amince da ita, wacce ta tabbatar da biyan albashin jami’an tsaron cikin gida har bayan ritaya.

Jami’an da za su samu wannan tagomashi sun shafi masu muƙamin mataimakin kwanturola, kwanturola, babban kwamanda zuwa sama.

Ministan ya sanar da hakan a Abuja, yayin taron tattaunawa da ministoci.

Dekta Tunji-Ojo ya ce shugaban ƙasar ya amince da sabuwar doka, wacce ta ba manyan jami’an tsaron damar ci gaba da karɓar albashi bayan sun yi ritaya.

Ministan ya ce, manufar wannan sabuwar doka ita ce inganta walwalar jami’an tsaro, kuma ta yi daidai da burin Shugaba Tinubu na daga darajar aikin ɗamara.

Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa ayyuka da inganta cibiyoyin gwamnati da ke a ƙarƙashin ma’aikatar harkokin cikin gida.

Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar FFS, DCF PO Abraham, ya fitar a ranar Alhamis bayan kammala taron.

A cikin sanarwar, ministan ya bayyana godiya ta musamman ga Shugaba Tinubu bisa goyon bayansa mara yankewa ga ma’aikatar.

Sanarwar ta ce, “Ministan ya nuna matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu saboda goyon bayansa da ba ya yankewa, yana mai tabbatar da cewa dukkanin hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar harkokin cikin gida suna cin gajiyar shirin Renewed Hope.”

Tunji-Ojo ya ce an riga an shafe dogon tarihin jinkirin ƙara wa jami’ai matsayi, inda ya bayyana cewa jami’ai fiye da 50,000 aka ɗaukaka matsayinsu cikin shekaru biyu kacal.

Ya kuma jaddada cewa a nan gaba, za a dawo amfani da sabon tsari, inda jami’ai za su samu ƙarin matsayi ne kawai bisa ingancin aiki da ƙwarewar da suka nuna.

Ministan ya kuma ce an ƙiƙiri sababbin takardun koyarwa, kuma ana kan gina sabuwar makarantar horar da ma’aikata mai suna Fire Academy, wacce za ta yi gogayya da manyan makarantun duniya, musamman kwalejin kashe gobara ta Arizona da ke Amurka.

Haka kuma, ya umarci hukumar kashe gobara ta tarayya da ta ƙara shiga haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu domin ƙara inganta ayyuka, gina sababbin gine-gine, da kuma zamanantar da harkokin kashe gobara a Nijeriya.

By ukarofi