Tinubu zai halarci taron rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ghana, Mahama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Litinin, 6 ga watan Junairu, 2025 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa Accra, Babban Birnin ƙasar Ghana domin halartar taron rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar, John Dramani Mahama wanda za a yi a ranar 7 ga wata.

Mahama shi ne ya zama Shugaban ƙasar na 12 a lokacin da aka zaɓe shi a shekarar 2011 zuwa 2017 wanda daga bisani a watan Disambar 2024 aka sake zaɓan sa inda zai gaji Nana Akuffo-Addo wanda ya jagoranci ƙasar daga 2017 zuwa 2025.

Shugaba Tinubu zai halarci taron ne bayan gayyata ta musamman da Mahama ya yi masa bayan ya ziyarci Nijeriya a watan Disamba saboda kyawawan alaƙoƙin da ke tsakanin shugabannin biyu da kuma ƙasashensu na tsawon lokaci.

Shugaba Tinubu, wanda shi ne shugaban hukumar shugabannin ƙasashen ECOWAS, zai samu rakiyar Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Misis Bianca Odumegwu-Ojukwu da wasu manyan jami’an gwamnati, kamar yadda Kakakinsa, Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

By ukarofi