Trump zai kori sojoji mata-maza a Amurka 

Ana sa ran zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka Donald Trump mai jiran gado zai zartar da wani umarni wanda zai kori sojojin Amurka, waɗanda mata-maza ne daga aikin soja da zarar an rantsar da shi, kuma a ranar dai ta farko akan karagar mulki.

An bayar da rahoton cewa, Trump yana shirya wata odar shugaban ƙasa, wacce da zarar an rantsar da shi a ranar 20 ga Janairu, 2025, wacce za ta hana mata-maza shiga aikin soja, sannan kuma a kori dubban masu canja halitta ta hanyar amfani da likitanci, waɗanda suka fara aiki a rundunar soja, inji jaridar Times.

Za a sallami waɗanda suka canza sheƙa ta halitta ta hanyar amfani da likitanci, wanda ke nufin za a sa su a layin “ba a yarda kuma ba za a amince” da su yi wa ƙasa hidimar aikin soja ba, inji jaridar Sunday Times da ta ambato jami’ai. 

Shugaban mai shekaru 78, a wa’adinsa na farko ya bayyana cewa, Amurka ba za ta ƙara “karɓa ko ba da izinin” shiga aikin soja ba, yana mai yin la’akari da tsadar magunguna da suke amfani da su. Ya rubuta a cikin 2017, yayin da haramcin ya fara aiki a 2019.