Batun sukar da Obasanjo ke yi wa gwamnatin shugaba Tinubu

Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya tayar da ƙura a kwanan baya lokacin da ya yi zargin cewa gwamnatocin da suka mulki Nijeriya a baya-bayan nan sun ci amanar al’umma, yana mai bayyana Nijeriya a matsayin “ƙasar da ta gaza”.

Da yake jawabi a taron Chinua Achebe a Jami’ar Yale, Connecticut, Amurka, Obasanjo ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su ba da fifiko wajen naɗa sabbin shugabanni masu aminci a Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) a dukkan matakai domin tabbatar da ingancin zaɓe.

Tsohon shugaban ƙasar, wanda ya yi magana a kan taken: “Rashin Jagoranci Nagari a Nijeriya,” ya bayyana abin da ke faruwa a ƙasar a halin yanzu a matsayin “Daƙile Hanyoyin Cigaba”.

Sai dai, mai ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi kakkausar suka ga kalaman Obasanjo, inda ya bayyana su a matsayin munafurci, inda ya ce kowa ya san Obasanjo da cakuɗa alƙaluma kuma ’yan Nijeriya ba za su ɗauki maganarsa ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a makon jiya, Onanuga ya ce mulkin Obasanjo ne ya jefa Nijeriya cikin tarin matsalolin da ake fama da su.

“Lokacin gwamnatin Obasanjo an samu cin hanci sosai amma kuma wai yau shi ne mai magana a kan rashawa,” inji hadimin shugaban ƙasar.

Ya ba da misali da batun tsige gwamnonin jihohi huɗu ba bisa ƙa’ida ba da kuma zargin cin hanci da rashawa da suka haɗa da yin amfani da kuɗaɗen gwamnati da kuma hannu a badaƙalar karɓar cin hanci da rashawa ta Halliburton.

Onanuga ya kuma soki yadda Obasanjo ya tafiyar da albarkatun tattalin arzikin Nijeriya a lokacin. Yayin da take amincewa da fa’idar kasafin kuɗi na hauhawar farashin ɗanyen mai a zamanin Obasanjo, sanarwar ta yi nuni da cewa an ɓarnata waɗannan damarmaki.

Hadimin shugaban ƙasar ya ce, a lokacin mulkin Obasanjo aka gurgunta dimokuraɗiyya a Nijeriya saboda neman mulki karo na uku.

Sunday Dare ya ce, tun da Obasanjo ya gama mulki ake ƙoƙarin share dattin da ya kawo Nijeriya wanda yanzu haka aikin da Tinubu ke yi kenan.

Dare ya ƙara da cewa, babu abin da zai kawar da hankalin Bola Tinubu daga ayyukan cigaba a Nijeriya a halin yanzu.

Manyan zarge-zargen da yake yi wa Obasanjo sun haɗa da yin watsi da ababen more rayuwa na ƙasa, da barin hanyoyin tarayya su lalace, da kasa magance matsalar wutar lantarki a ƙasar duk da kashe dala biliyan 16 wajen ayyukan wutar lantarki.

“Obasanjo ya gaza gyara munanan hanyoyin gwamnatin tarayya ko kuma faɗaɗa hanyoyin sadarwa na ƙasa,” inji sanarwar, inda ta lissafo ayyukan da ba a kammala ba kamar babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Har ila yau, ya zarge shi da ba da fifiko ga buƙatun kansa, kamar inganta kamfanoni masu zaman kansu kamar jami’arsa da ɗakin karatu na fadar shugaban ƙasa, wanda aka ba da kuɗi ta hanyar gudunmawar da ake tuhuma.

Har ila yau, an soki yunƙurin Obasanjo na mayar da hannun jari a matsayin wanda ke cin gajiyar wasu makusantansa wajen kashe muradun ƙasa.

Onanuga ya bayyana cece-kuce na sayar da Kamfanin Aluminum Smelter Company of Nigeria (ALSCON) a kan ɗan kaɗan daga darajarsa, a matsayin babban misali.

Sanarwar ta kuma yi Allah-wadai da neman wa’adi na uku na Obasanjo, wanda aka bayyana a matsayin “aikin da ya gaza” wanda ya salwantar da biliyoyin Naira.

Ya yi nuni da cewa kura-kuran tsarin zaɓen da ya gudanar a shekarar 2007 ya gurgunta masa kwarin gwiwa na yin tsokaci a kan mulki da ingancin zaɓe.

Bugu da ƙari, ana zargin Obasanjo da yin sakaci a harkar tsaron ƙasa a lokacin gwamnatinsa, wanda hakan ya sanya sojojin ƙasar ba su da kuɗaɗe da kuma rashin kayan aiki.

Sanarwar ta yaba wa gwamnatocin jam’iyyar APC da suka biyo baya wajen inganta aikin sojan Nijeriya da inganta ayyukan tsaro.

Daga karshearshe ya buƙƙci Obasanjo da ya maida hankali wajen goyon bayan Tinubu maimakon suka.

Obasanjo ya yi ƙaurin suna kan sukar gwamnatin Tinubu, inda Sanata Jimoh Ibrahim, mai wakiltar Ondo ta Kudu, jihar Ondo ya buƙaci tsohon shugaban ƙasar da ya daina yin kalamai masu tayar da hankali yayin da yake tsokaci kan halin da ƙasa ke ciki.

Sanatan ya shawarci Obasanjo da ya kula da harcensa, yana mai cewa yin amfani da harshen yaƙi a lokacin zaman lafiya tamkar tada zaune tsaye ne.

Ibrahim, wanda ya yi magana a wani shirin talabijin, ya ce saɓanin ikirari na Obasanjo, Nijeriya ba ƙasa ce ta da gaza ba.

“Ina matuƙar girmama tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, amma harshen yaƙi a lokacin zaman lafiya bai dace ba.

Duk gwamnatin bayan Obasanjo ta sha wahala daga tsohon shugaban ƙasa, wanda ya kamata ya zama uba. Bayan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Obasanjo ya samu gatan da ba kasafai ba na mulkin Nijeriya a matsayinsa na shugaban ƙasa na soja da kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na dimokraɗiyya na tsawon shekaru 11.