Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani sabon tashin hankali yana faruwa yayin da tsagerun yankin Neja Delta ke sake zama da shirin kai sabbin hare-hare.
Wani rahoton sirri da ya nuna cewa shugabannin tsagerun sun taru a wani rafi da ba a bayyana ba don tsarawa tare da daidaita hare-haren gama-gari kan cibiyoyin mai, wanda hakan ya haifar da sabon tashin hankali a yankin Neja Delta a ƙarshen mako.
Taron ya zo ne kwanaki kaɗan bayan da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ta hanyar ayyana dokar ta-ɓaci a ranar Talatar da ta gabata.
Ba a bayyana cikakken bayani ba, sai dai wata majiya mai tushe ta ce shugabannin tsagerun na son tabbatar da cikakken haɗakar ƙungiyoyin tsagerun Neja Delta daban-daban kuma suna tattaunawa kan tsayar da shugaban ɗaya.
Kwamanda Bibi Oduku, babban kwamandan Rundunar Tsaro ta Riɓerine (Coast-Guard of the Federation), wanda ya tabbatar da babban barazana a yankin Neja Delta da kuma tasiri hakan kan tattalin arzikin Nijeriya, ya shawarci Shugaba Tinubu da ya sake yin la’akari kan batun dakatar da Fubara.
Ya ce, “Ina kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yi la’akari da dakatarwar da aka yi wa gwamnan jihar Ribas saboda tashe-tashen hankula da barazana a yankin Neja-Delta, waɗannan barazanar na da matuƙar haɗari ga tattalin arzikin ƙasa.
“ƙungiyoyin ’yan bindiga na shirin kai hari kan kadarorin gwamnatin tarayya a faɗin jihar Neja Delta yayin da ɓata-gari na iya yin amfani da lamarin wajen aikata miyagun laifuka.
“Wannan na iya haifar da asarar rayuka a tsakanin ‘yan ƙasa da ba su ji ba ba su gani ba da kuma jami’an soja da aka tura domin wanzar da zaman lafiya.
Kwamanda Oduku, ya bayar da tabbacin cewa, “Jami’an tsaron kogin suna taka-tsantsan kuma a shirye suke su hana ƙungiyoyin da ba su da izini shiga ayyukan da ba su dace ba, kuma za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro domin kamo waɗanda ke da hannu wajen kai hare-hare kan kadarorin gwamnatin tarayya.”
Haka kuma, Kyaftin Eric Foutoru da ThankGod Oprom da ke kula da magudanar ruwa na jihohin Ribas da Delta, sun yi alƙawarin tallafa wa sojoji wajen kwantar da hankulan al’amuran tsaro a jihohin da yankin Neja Delta baki ɗaya.
Oduku ya tuna da kalaman tsohon mai baiwa shugaban ƙasa, Birgediya Janar Paul T. Boroh (mai ritaya), wanda ya gargaɗi matasa a yankin Neja Delta da kar da su bar fushi ya karkata akalar ayyukansu.
“Shugaba Tinubu ba mai son tashin hankali ba ne, don haka ya kamata matasa su guji aikata haramtattun ayyuka da za su iya cutar da rayuka da dukiyoyi.”
Ya yi Allah-wadai da lalata bututun mai a jihohin Ribas da Akwa Ibom, inda ya yi alƙawarin cewa jami’an tsaron kogin za su gurfanar da masu aikata laifin a gaban kotu.
