Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mai Martaba Sarkin Kano, Lamiɗo Sanusi, ya roƙi jama’ar jihar da su kasance masu bin doka da oda, kuma su guji ayyukan da ka iya tada tarzoma a birnin.
Ya la’anci masu adawa da mayar da shi sarki, yana mai cewa wuta za ta cinye masu ƙoƙarin cinnawa birnin wuta.
A cikin wata sanarwa da ta fito daga harshen Hausa da Firimiya Radio a Kano ya wallafa a shafin Facebook a ranar Litinin, Sarki Sanusi ya ce masu ƙalubalantar masarautarsa suna ƙalubalantar ikon Allah kuma ba za su ƙare lafiya ba.
“Muna kira ga jama’a da su kasance masu bin doka da oda, wannan rikicin Masarautar ba ni su ke ba, suna faɗa da abin da Allah Ya ƙaddara zai faru, Allah ba Ya buƙatar taimakon kowa, ina roƙon ku da ku yi haƙuri, Allah zai ci gaba da tallafa wa masu adalci.
“Wuta za ta cinye duk wanda ke shirin cinna wuta a Kano, kada ya taɓa shaida zaman lafiya a rayuwarsa, Allah Ya tsare mana ƙasarmu da rayukanmu, In Sha Allahu duk wanda ke ƙalubalantar hukuncin Allah ba zai ƙare lafiya ba,” inji Sarki Sanusi.
Wataƙila hakan ba ya rasa nasaba da tashin hankalin da ake fama da shi a jihar biyo bayan umarnin da gwamna Abba Yusuf ya bayar ga majalisun masarautun jihar a ranar Talata na fara shirye-shiryen Hawan Sallah.
Biyo bayan umarnin gwamnan, abokin hamayyar Sanusi, Aminu Ado Bayero, ya kuma sanar da jami’an tsaro aniyarsa ta gudanar da wata Hawa a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun sakataren sa Abdullahi Kwaru.
Wasiƙar ta ce Alhaji Ado Bayero zai yi bikin cika shekaru biyar a matsayin Sarkin Kano.
“Manufar wannan wasiƙa ita ce sanar da jami’an tsaro a jihar Kano, musamman rundunar ‘yan sanda a hukumance, bikin Sallah na wannan shekarar ya zo daidai da cikar mai martaba sarki na kakanninsa shekaru biyar tare da ba da tabbacin cewa za a gudanar da dukkan ayyukan Hawan Sallah cikin lumana,” inji Ado Bayero.
Mutanen biyu dai sun ɗau sarauta ne tun bayan da gwamnatin jihar ta tsige Ado Bayero a watan Mayun da ya gabata tare da mayar da tsohon sarkin da ya gada, Sanusi, bisa wata sabuwar dokar masarautu.
