Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fadar Shugaban ƙasa ta yi watsi da ikirarin dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da wasu ‘yan siyasa a Jihar Ribas wani yunƙuri ne na kwace mulki, inda ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki matakin da ya dace ne don hana jihar faɗawa cikin rikici.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Lahadi, inda fadar shugaban ƙasar ta bayyana buƙatar gaggawar shiga tsakani.
A cewar sanarwar, rashin basiri ne a jira rugujewar mulki gaba ɗaya kafin a shiga tsakani.
Fadar shugaban ƙasa ta dage cewa rikicin Ribas, wanda ya samo asali daga taƙaddamar mulki tsakanin Gwamna Fubara da ‘yan majalisar tarayya masu biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya gurgunta harkokin mulki.
Ta yi nuni da cewa, duk da hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da tsarin mulkin ƙasa, ɓangarorin da ke gaba da juna sun ƙi ja da baya, suna mai jaddada cewa “rahotanni na leƙen asiri sun tabbatar da cewa tsegerun Neja-Delta sun yi dafifi wajen yin zagon ƙasa ga muhimman ababen more rayuwa na mai, wanda ke yin barazana kai tsaye ga tsaron tattalin arzikin Nijeriya.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ka yi tunanin jihar Ribas inda Shugaba Tinubu ya yi jinkiri. Rikicin siyasa zai iya haifar da rikici, tare da kai hare-hare a kan ‘yan majalisar dokoki da kuma muhimman abubuwan da ke tattare da man fetur na jihar. Za a rufe makarantu da asibitoci, masu zuba jari za su gudu, kuma asarar mutane da tattalin arziki za su zama ruwan dare.
“Ya zuwa ranar 18 ga Maris, lamarin ya taɓarɓare fiye da ƙudurin siyasa, wanda hakan ya sa ba za a iya kaucewa shiga tsakani na Shugaban ƙasa ba.”
Fadar shugaban ƙasar ta ƙara da cewa, yayin da masu sukar lamirin ke cewa dakatarwar da aka yi wa Gwamna Fubara da sauran ‘yan siyasa cin zarafi ne ga dimokuraɗiyya, amma matakin wani sabon salo ne na wucin gadi, ba wai wani abu ba ne.
“Wannan ba wani ƙarfin iko ba ne, shiga tsakani na wucin gadi ne, da nufin maido da cibiyoyi na dimokuraɗiyya – ba maye gurbinsu ba. An tsara dakatarwar na tsawon watanni shida don kwance ɗamarar ɓangarorin da ke rikici da juna da daidaita harkokin mulki.”
Har ila yau, ta yi nuni da munafuncin wasu masu suka da suka yi shiru kan ƙin ba Fubara haɗin kai da majalisar dokoki, amma duk da haka sun yi Allah wadai da matakin na shugaban ƙasar.
A cewar sanarwar, “Dimokraɗiyya ba za ta iya ci gaba a cikin rashin bin doka ba – rashin bin doka ya saɓa wa doka.”
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya (Sashe na 305) ya bai wa shugaban ƙasa ikon yin aiki a lokacin da al’ummar ƙasar ke fuskantar taɓarɓarewar doka da oda da kuma tattalin arzikin ƙasa – daidai abin da ke faruwa a Ribas.”
Fadar shugaban ƙasa ta yi tsokaci kan abubuwan tarihi da suka haɗa da dokar ta-ɓaci da ta gabata a Filato da Borno, don tabbatar da matakin da Tinubu ya ɗauka.
