Tsaleliyar budurwa ta yi wuf da Sarkin Daura bayan soyayyar mako guda

Daga AISHA ASAS a Abuja

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya auri wata tsaleliyar budurwa ’yar shekara 22 mai suna Aisha Yahuza Gona mako guda bayan fara soyayyarsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an ɗaura auren ne a garin Safana da ke Jihar Katsina a cikin yanayi na rashin tara ɗimbin jama’a a wajen shagalin, duk da cewa, amaryar ɗiya ce ga tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Safana, Alhaji Yahuza Gona.

An bayar da rahoton cewa, Mar Martaba Sarkin, wanda a farkon shekarar nan ya yi bikin cikarsa shekara 15 a gadon sarauta, ya auri ’yar shekara 20 cikin watan Disamba, 2021, inda ya biya sadakin Naira Miliyan guda tsaba, kasancewar ɗiya ce ga wani basarake a Katsina.

Yanzu haka dai Mai Martaba Umar Faruk, mai shekaru 91 da haihuwa, tuni ya tare da zankaɗeɗiyar amaryarsa. Allah ya kawo ƙazantar ɗaki!