Yaushe Ganduje zai zartar da hukunci kan makashin Hanifa? …Bayan kotun Kano ta yanke wa makashin Hanifa hukuncin rataya

*Lokacin da gwamna ke da ikon saka hannu kan hukuncin – Lauya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A jiya ne Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 6 da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako da ke Birnin Kano a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Usman Na’abba ta yanke wa malamin makarantar nan da aka kama da aikata laifin kisan ɗalibarsa, Hanifa Abubakar, wato Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun sa da laifin yin garkuwa da ita da kuma kisan ta.

Haka kuma kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyar, saboda samun sa da laifin haɗa baki da kuma ɓoye ta.

Shi ma Hashim Isyaku, wanda aka tuhuma da laifin haɗa baki da taimaka wa Abdulmalik Tanko wajen binne gawar Hanifa, kotun ta yanke masa hukuncin kisa da kuma hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan gyaran hali. 

Haka kuma kotun ta yanke wa budurwar Abdulmalik, Fatima Jibril Musa, hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan gyaran hali, saboda samun ta da laifin haɗa baki da kuma yunƙurin yin garkuwa.

Yayin yanke hukuncin, Mai Sharia Na’abba ya ce, kotun ta yanke wannan hukunci ne bisa gamsuwa da shaidu da hujjoji da masu gabatar da ƙara suka gabatar a gabanta. 

Tun da farko mai gabatar da qara Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya nemi kotun da ta yanke wa waɗanda ake tuhuma hukunci mai tsanani daidai da laifin da suka aikata.

Sai dai lauyoyin waɗanda ake ƙara ƙarƙashin jagorancin, Barista Asiya Imam, sun nemi kotun ta sauƙaƙa wa waɗanda ake tuhuma kasancewar suna da iyali waɗanda nauyinsu ya rataya akansu.

Haka kuma a cewar lauyoyin wacce ake tuhuma ta uku, Fatima Jibril Musa uwa ce da ke da ƙaramin goyo. 

Idan za a iya tunawa tun a ranar 24 ga Janairu 2022, Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Abdulmalik Tanko mai shekara 34 da Hashim Isyaku mai shekara 37 da kuma Fatima Jibril, dukkaninsu mazauna unguwar Tudun Murtala a gaban kotun bisa zarginsu da aikata laifuka guda huɗu da suka haɗa da haɗa baki da na garkuwa da na ɓoyewa da kuma na kisa, laifukan da suka saɓa da sashe na 97 da na 274 da na 277 da na 221 na kuɗin shari’a na final Kod.

Takardar ƙarar ta bayyana cewa, a ranar 4 ga watan Disamba 2021, Abdulmalik Tanko wanda malamin makarantar Noble Kids School da Hanifa Abubakar ’yar kimanin shekara biyar a duniya, ya sace ta tare da ɓoye ta a daidai lokacin da ta ke dawowa daga makarantar Islamiyya, inda ya ajiye ta a gidansa tsawon kwana shida.

“Daga bisani ya nemi kuɗin fansa Naira miliyan shida daga mahaifanta, inda ya fara karɓar N100,000 a matsayin somin taɓi.

Takardar ƙarar ta ci gaba da cewa, “Bayan wasu kwanaki Abdulmalik ya kashe Hanifa ta hanyar ba ta shinkafar ɓera, inda kuma ya haɗa kai da Hashim Isyaku ya binne ta a wani ɓangare na wata makarantarsa Northwest Preparatory Scholol da ke unguwar Tudun Murtala bayan ya gutsttsura gawarta ya ɗure a cikin buhu.”

Sai dai waɗanda ake zargi sun musanta aikata laifin kisan, inda suka amince da laifin haɗa baki da yin garkuwa da kuma ɓoye Hanifa.

Wannan shari’a ce wacce ta ja hankalin al’umma ƙwarai da gaske, inda ake ta kiraye-kiraye kan a tabbatar da adalci kan ran Hanifa da aka salwantar.

Tuni dai Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da cewa, da zarar an yanke wa Tanko hukuncin kisa, gwamnan ba zai yi kasa a gwiwa wajen rattava hannu, don aiwatar da hukunci ba nan take. Wannan furuci na Gwamna Ganduje ya ja hankalin al’umma, saboda yadda suka ƙagu su ga an bi kadin rayuwar Hanifa, ɗalibar da ba ta ji ba, ba ta gani ba.

A yanzu kallo ya koma sama, don ganin gwamnan ya cika alƙawarin da ya ɗauka tunda na yanke hukunci.

Blueprint Manhaja ta nemi jin ta bakin Kwamishinan Labarai na Jihar Kano, Kwamred Muhammad Garba, don jin inda aka kwana kan wannan alwashi da Ganduje ya ci. To, amma har zuwa wallafa wannan rahoto bai amsa kiran waya ba kuma bai amsa saƙon da aka tura masa a wayar ba.

Sai dai kuma, duka da haka, Blueprint Manhaja ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen jin ta bakin ƙwararru kan harkokin shari’a ba. Barista Nazir Adam ya shaida wa Blueprint Mahjaa cewa, gwamna ba zai iya rattaɓa hannu kan hukuncin kisa ba har sai wanda aka yanke wa ya kammala bin kadin haƙƙinsa na ɗaukaka ƙara.

Barista Adam ya ce, wanda aka yanke wa hukuncin yana da kwanaki 90 na ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, sannan yana da wasu ƙarin kwanakin na sake ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli. Ya ƙara da cewa, sai bayan Kotun Ƙoli ta yi nata hukuncin ne gwamna ke da ikon sa hannu kan hukuncin, idan ta tabbatar da shi.

Yanzu dai za a jira a gani ko Abdulmalik Tanko da sauran waɗanda aka yanke wa hukunci za su ɗaukaka ƙara ko kuwa dai akasin hakan!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *