Kasuwanci ɓangaren da ba na masana’antun ƙira ba a Sin ya ci gaba da farfaɗowa a watan Yuli

Daga CMG HAUSA

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar jigilar kayayyaki da ta masu sayayya ta ƙasar Sin da cibiyar binciken ayyukan hidima ta hukumar ƙididdiga ta ƙasar, sun sanar a yau Lahadi da cewa, alƙaluman harkokin kasuwanci da ba na masana’antun kira ba, sun kai kaso 53.8 bisa ɗari a watan Yuli, adadin ya ƙaru da kaso 0.5 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin a bara, wato ya kai sama da matsakaicin matsayin rabin farkon bana.

Alƙaluma game da ma’aikatan harkokin kasuwancin ba ta sauya sosai ba, kuma ayyukan hidima na ci gaba da farfaɗowa. A taƙaice dai, ana iya cewa, harkokin kasuwanci da ba na masana’antun kira ba a ƙasar Sin, suna ƙara farfaɗowa sakamakon manufofin gwamnatin ƙasar da raguwar tasirin annobar COVID-19.

Ban da haka, ana samar da guraben ayyukan yi a fadin ƙasar yadda ya kamata, kana matsin lambar da kamfanoni ke fuskanta yana ƙara sauƙaƙa. Haka kuma, ana samun ƙaruwar zuba jari, sannan ana sayar da hajoji lami lafiya, bugu da ƙari, aikin hidima dake buƙatar cudanyar mutane yana farfaɗowa cikin sauri.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa