Tsarabar taron marubutan Hausa a Kano

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Allah cikin ikonSa Ya bani damar halartar Babban Taron Marubutan Hausa da aka gudanar a birnin Kano, wanda ya samu halartar marubuta, manazarta, malaman jami’o’i da ‘yan jarida da dama daga sassan Nijeriya daban-daban. An shirya taron ne da nufin samar da muhallin da tsofaffi da fitattun marubuta za su gana da matasan marubuta na yanar gizo, da kuma tattauna hanyoyin da za a bi a tallafawa ƙananan marubuta masu ƙwazo da ke da burin shiga sahun manyan marubuta, don ganin sun samu ƙwarewar da suke buƙata a fagen rubuce rubucen fim, labaran hikaya, da Gasar Gajerun Labarai.

Taron wanda aka yi wa taken “Marubuta Da Cigaban Zamani,” ya haɗo kan tsofaffin marubuta littattafan Hausa waɗanda yanzu su ne fitattun masu rubutun finafinai gajeru da masu dogon zango da ake fitarwa a tashoshin talabijin da manhajar YouTube, irin su Nazir Adam Salihi, Nasir Ibrahim NID, Fauziyya D. Suleiman, Maimuna Idris Sani Beli, da sauran su, waɗanda suka faɗakar da mahalarta taron yadda canjin zamani ya riski harkar rubutun adabi sakamakon komawar rubutu kafafen sadarwa na yanar gizo, da shirin da ake yi na zaƙulo wasu daga cikin matasan marubuta da ke da sha’awar shiga harkar rubutun labaran fina-finai, domin fara shirya musu baitoci da haɗa su da masu ɗaukar nauyin shirya finafinai, don su ma a fara jin amon su da kuma gwada irin baiwar ƙirƙirar labari da suke da ita. Kamar yadda wasu daga cikin su ke neman samun irin wannan damar, kuma suke bibiya da nuna nacin a saka su a hanya.

An yi amfani da taron wajen ƙara wa juna sani daga shugabannin taron da wasu marubutan yanar gizo da aka fi sani da marubutan online, waɗanda kowannen su ya ja hankali game da buƙatar nuna jajircewa, haquri, kiyaye ƙa’idojin rubutu da rungumar fasahar zamani don cin ribar sauyin kasuwancin littattafai da finafinai a wannan zamani.

A cikin jawabinsa marubuci Nazir Adam Salihi ya bayyana bambancin tsofaffin marubuta da matasan marubuta na online, wanda daga ciki ya nuna cewa marubutan baya na da tsananin kiyayewa wajen amfani da kalmomin batsa cikin rubutun su, amma a cikin marubutan zamani ana samun yawaitar hakan. Don haka ya buqaci a riqa samar da tsaftar rubutu, da tuntuvar abokan rubutu ko manyan marubuta, domin neman shawara kan yadda za a inganta rubutun da ake so a yi ko ake kan yi.

Ya ce, idan marubuci yana sha’awar yin rubutu kan wani jigo da yake ganin yana da muhimmanci to, ya yi nazari da kyau wajen neman sanin yadda girman matsalar take a cikin al’umma. Domin a cewarsa ba a ɗaukar jigon rubutu daga abin da bai zama gama gari ba, sai abin da ya zama ya buwayi jama’a, ta yadda za a yi rubutu a kai domin faxakarwa da samar da gyara.

A kan bambancin marubutan da da na yanzu, Malam Nazir ya ce, a tsakanin rukunin marubuta na baya akwai matuƙar girmama juna da taimakawa, saɓanin yadda marubutan yanzu suke samun yawan ƙalubalantar juna da yawo da ƙananan maganganu. Shi ya sa ya ba da shawarar lallai a riƙa martaba juna, kuma a riqa ba da uzuri, ana haquri a lokacin da ake neman haɗin kai da taimakon tsofaffin marubuta, saboda hidindimu da suke yi musu yawa, ba zai yiwu a samu yadda ake so ba a lokaci guda ba, sai an yi haƙuri. Ba don girman kai ko wulaƙanci ba ne, kamar yadda wasu a cikin matasan ke ɗauka. Sai dai ya qarfafa cewa, yana da kyau marubuci ya jajirce sosai wajen nuna kansa, da irin baiwar da yake da ita, da kuma nacinsa wajen ganin ya yi zarra a harkar rubutun adabi, domin ta haka ne za su iya saurin gano ƙoƙarin marubuci, da ba shi damar cin ribar damarmakin da ake samu a harkar rubutu.

Wani ƙalubale da matasan marubutan Hausa ke fuskanta ita ce ta rashin fahimtar yadda za su tunkari Gasar Gajeren Labari da ƙungiyoyi, kamfanoni da tashoshin rediyo daban-daban ke shiryawa, musamman ma dai Gasar Hikayata ta BBC Hausa. Marubuta da dama suna kokawa da yadda suke wahalar samun nasara a gasar, duk kuwa da yadda suke ganin suna ƙure ƙoƙarinsu da basirarsu. Fitacciyar marubuciya kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka tava samun nasara a Gasar Hikayata, Maimuna Idris Sani Beli ta gabatar da lacca game da dabarun da ake bi don cin nasara a gasar marubuta, inda ta bayyana muhimmancin marubuta su nuna kulawa da damuwa wajen sanin abubuwan da suka shafi rayuwa da al’amuran yau da kullum a kewayensu, kuma su san yadda ake dogon labari da gajeren labari, don su iya rubutu a fagage daban-daban da za a iya buƙatar yin rubutu a kansu.

Ta ce, a duk lokacin da aka sanya gasa, lallai marubuci ya nazarci ƙa’idojinrubutu, da sanin dokokin gasar.

Wannan faɗakarwa da ta yi ya samu goyon bayan Farfesa Yusuf Muhammad Adamu, wanda ya shawarci marubuta su san manufar da suke son yin rubutu a kansa. Sannan tilas kowanne marubuci ya san ƙa’idojin rubutu, da burin da yake son cimma a rubutunsa. Ya riƙa neman masana ko waɗanda suka gabace shi a rubutu don a duba masa, kuma ya yi haƙuri ya jira a duba masa da kyau. Kowanne marubuci ya sani cewa duk da kasancewar rubutu baiwa ce, amma yana buƙatar nazari da bincike, don inganta saqon da ake so a isar ga jama’a.

Ita ma marubuciya Fauziyya D. Suleiman da ta gabatar da takarda mai taken, “Daga Baƙuwa Zuwa Tauraruwa”, ta yi bayani kan tarihin gwagwarmayarta a duniyar marubuta, daga yadda ta fara a matsayin baƙuwar marubuciya har zuwa matakin da yanzu ta zama abar koyi ga mata marubuta da dama. Ta bayyana irin matakan da marubuci ke buƙata ya taka don samun nasara da ɗaukakar da ya ke neman ya samu.

Ta nuna cewa rashin basira ce ke sa wasu marubuta amfani da batsa don tunanin riƙe mai karatu ko samun ɗaukaka, wanda hakan ke zama na wani taƙaitaccen lokaci. Amma marubutan batsa ba sa tasiri, kuma ba sa shahara ko ɗaukar hankalin duniya. A duk lokacin da wata ƙungiya ko kamfani yake neman kwararrun marubuta, ba a tunaninsa marubutan batsa a ciki. Ta ce, dole sai marubuci mai son shahara ya nace da bibiyar masana don samun shawarwari na yadda zai inganta rubutunsa. Sannan ta bayyana burin da tsofaffin marubuta ke da shi na samar da tsarin yadda za a riƙa ba da horo da koyar da sabbin marubuta na online, yadda za su samu ilimi da dabarun rubutun fim da sauran ayyukan rubutu da ake buƙata.

Fitaccen mawaƙin nan kuma tsohon marubuci, Aminu Ladan Abubakar mai laƙabi da ALA ya yi farinciki da jin wannan albishir inda ya ƙarfafa gwiwar manyan marubutan lallai su jawo matasan marubutan nan a jiki, su koya musu sirrin da suke da buƙatar sani don su samu gogewa da sanin dabarun inganta rubuce-rubucensu, a matsayin su na manyan gobe, waɗanda harkokin rubutun za su koma wajensu.

Taron ya samu halartar wasu fitattun masu shirya finafinai na masana’antar Kannywood, waɗanda ke aiki kafaɗa da kafaɗa da marubuta da ke samar musu da labaran da suke shirya fim a kansa, ko tsara labarin da suka qirqira ta yadda zai ja hankalin masu kallo. Furodusa Abdul Amart Maikwashewa, Umar UK Entertainment, Falalu Ɗorayi, Malam Tijjani Shehu Bala da sauran su, sun bayyana aniyarsu ta yin aiki da matasan marubutan da suka yi zarra kuma suka ƙware wajen iya sarrafa labari da tsara labarin fim, don cigaba da inganta sana’arsu.

Sai dai a ra’ayin marubuci, ɗan jarida kuma ɗan siyasa, Malam Aliyu Samba bai kamata a jira sai lokacin da waɗannan matasan marubuta suka gama samun ƙwarewa sannan za a shigar da su cikin manyan ayyukan rubutu ba. A cewarsa, gwaji ne yake kai mutum ga samun ƙwarewa, idan ba a ba su dama ta yaya za a san sun ƙware ko za su iya?

Dangane da batun da ya shafi cigaban kasuwancin littattafai Darakta Falalu Ɗorayi ya tunatar da marubuta yadda a farkon fitowar harkar ɗora littafi a yanar gizo, marubuta ne suka fara cin gajiyar tsarin kafin ‘yan fim su shigeta, amma sai gashi an bar marubuta a baya. Ya ƙalubalanci marubuta su rungumi hanyoyin da fasahar zamani ta kawo wajen tallata littattafansu a yanar gizo, kamar yadda ‘yan fim ke cin kasuwarsu a YouTube. A kan wannan muhimmin batu ne kuwa matashiyar marubuciya Na’ima Suleiman Sarauta mai laƙabi da NimcyLuv ta gabatar da jawabi mai taken Hanyoyin Sayar Da Littattafai a Online inda ta ƙarfafa wa marubuta gwiwa kan ɗaukar rubutu a matsayin sana’a ba sha’awa ba kawai, domin ta haka ne za su samu ƙwarin gwiwa da bunƙasa a harkar rubutun da suke yi.

Wani abu da ya ja hankalina a bayanan da aka gabatar, dangane da cigaban kasuwancin littafi shi ne wata shawara da wani marubuci mai shirya finafinai Tijjani Shehu Bala ya bayar, inda ya buqaci marubuta su rungumi sabuwar fasahar nan Artificial Intelligence, wajen yin rubuce-rubuce da kasuwancin littattafai, don tafiya da zamani. Kodayake marubuci Aliyu Samba ya ja kunnen marubuta ahir ɗin su da yin saki na dafe da baiwar da Allah ya ba su ta ƙirƙira, domin kuwa irin waɗannan fasahohi na zamani suna da iyakar abin da suke iya yi wa mutum, ba abin dogaro ba ne, duk kuwa da kasancewar suna da amfanin da za a iya mora.

Sadiya Kazaure mai laƙabi da SADNAF, da Ummul-Khairi Sani, daga ɓangaren marubutan online sun yi magana game da muhimmancin haɗin kai da ƙalubalen da rubutun batsa ke haifarwa ga marubutan online.

Babu shakka masu shirya wannan taro sun cancanci a yaba musu bisa amsa kiraye-kiraye da suka yi, da jajircewa da niyyar alheri da suka ƙudurta a ransu na horar da matasan marubuta da ba su damar da za su fitar da kansu ga duniya. Da fatan su kuma marubutan da aka yi abin domin su za su ba da haɗin kai, a yi abin da ya kamata, domin cimma nasarorin da ake so a cimma.

Sannan zan yi roƙo idan wannan dama ta zo a tuna da marubuta na sauran jihohi da suke wajen Jihar Kano.