NAGARI NA KOWA: Tasirin Muhammad Nami a Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS)

Daga NKEM PRECIOUS
(Fassarar Abubakar Salisu)

Lambobin yabo guda biyu da Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS) ya samu a wurare biyu kwanan nan, sun nuna irin muhimmaci da ƙwazon da ya ke da shi da kuma jajircewa kan aikin da aka ɗora masa na tattara kuɗaɗen haraji.

Lambar yabo ta farko ita ce Kyautar Gwarzon Cibiyar Akantoci ta Najeriya (ICAN), wadda aka ba shi a ranar 6 Ga Mayu, 2023.

Nagarta da sanin ya kamata ya sa shi kuma Nami ya sadaukar da wannan muhimmiyar lambar yabo da ya samu ga dukkan ‘yan ajin su da su ka yi karatu tare, tun daga firamare har zuwa jami’a. Haka kuma Nami ya haɗa har da abokan aikin sa na cikin Kwamitin Shugaban Ƙasa Mai Ƙididdige Kadarorin Satar da Gwamnatin Tarayya ta Ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati, mambobin Kwamitin Bayar da Shawara kan Tattara Haraji, dukkan masu biyan haraji da mabobin Hukumar Gudanarwar FIRS da ma’aikatan hukumar. Duk Nami ya haɗa har ma da iyalan sa, duk ya sadaukar da wannan lambar yabo gare su.

Nami nagartaccen mutum ne kuma jajirtaccen da ya samu ingantaccen horo wajen iya tattara kuɗaɗen haraji. Kuma ya samu lambar yabo ta Gwarzon Ƙwarewar Aiki ta jaridar BusinessDay.

Tun bayan da ya zama Shugaban Hukumar FIRS cikin 2019, Nami ya kasance ya na aikin sa cikin natsuwa tare da samun cimma ƙudirorin da gwamnati ke so a cimma. A cikin waɗannan ‘yan shekaru ya ƙarar wa shugabancin FIRS karsashi ta hanyar samar da ci gaba sosai a hukumar.

A babban taron karrama shi da Lambar Yabo ta ICAN a lokacin taron ICAN na shekara-shekara a Legas, ranar Asabar 6 Ga Mayu, Shugaban ICAN Tijjani Isa ya bayyana cewa Nami mutum ne da ya yi ƙoƙarin samun nasarar ciyar da FIRS a gaba a cikin ƙasa da kuma duniya, duk kuwa da irin ƙalubalen da duniya ta fuskanta na matsalar tattalin arzikin ƙasashe.

Shugaban na ICAN ya ce Nami ya cancanci babbar lambar yabon da ICAN ta ba shi, saboda gagarimar gudummawar da ya bayar, kuma ya ke kan bayarwa a haɓɓaka tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar ƙasar nan.

Manya-manyan tsare-tsaren inganta rayuwar da Nami ke bijiro da su a FIRS ne su ka maida hankalin ICAN har ta gamsu cewa Nami ya cancanci yabo.

A wurin irin wannan taron bayar da lambar yabo na BusinessDay a ranar 4 Ga Mayu kuma, jaridar ta bayyana cewa Nami ya cancanci lambar yabo da ya samu ne saboda irin hangen nesan da ya kawo wajen haɓɓaka ayyukan Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS).

Nami ya Inganta tsarin karɓar kuɗaɗen haraji da kuma tabbatar da cewa ana samun ɗorewar masu biyan harajin da kuma ɗorewar karɓar tara kuɗaɗen.

Shigo da tsarin TaxPro Max ya samar da hanya mafi sauƙi ta fasahar zamani, inda masu biyan haraji ke rajista da biyan harajin su ta cikin manhaja ko daga ina su ke, ba sai a ofishin FIRS ba.

TaxPro Max ta ƙawar da matsanancin jinkirin da ake samu biyan kuɗin haraji a baya, lamarin da a wannan lokacin ya riƙa haifar da jinkiri wajen biya da tara kuɗaɗen haraji da kuma sulalewar maƙudan kuɗaɗen haraji.

BusinessDay ta jinjina wa Nami wajen ƙoƙarin sa na inganta ayyukan ma’aikatan FIRS tare da shigo da na’urorin fasahar zamani wajen tabbatar da gudanar da aiki da gaskiya, bin-diddigi da kuma samun kyakkyawar nasara.

Da ya ke godiya wurin ba shi lambar yabo, Nami ya ce, “Tun bayan da na kammala digirin farko a jami’a shekaru 32 da su ka gabata, na samu sa’ar yin kusanci da mambonin Cibiyar ICAN, yanzu ga shi har ta kai ni ina aiki kai-tsaye da mambobin ICAN fiye da 3,000, a matsayi na na Shugaban Hukumar FIRS.”

Nami ƙwararre ne wajen bayar da shawarwari ga masu zuba jari musamman a sabbin-shigar harkokin kasuwanci da hada-hadar kuɗaɗe.

Nami ya fara aiki da PKF a cikin 1993 inda har ya kai ga babban matsayi. Ya rike muƙamai daban-daban a wurare daban-daban a fannonin hada-hada da bin-diddigin kuɗaɗe.

Iya aiki, gaskiya da riƙon amanar sa ce ta sa a shekarar 2022 Hukumar FIRS ta tara maƙudan kuɗaɗen harajin da ba ta taɓa tara kamar su a cikin shekara ɗaya ba, har naira tiriliyan 10.1.

Sauƙin kan sa, iya aiki, gogayya da kuma amana da kishin ƙasa su ne kyawawan ɗabi’un da ke ci gaba da kai Nami a matakan nasara bisa turbar kyakkyawan tsarin shugabancin da ya ke yi wa Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS).

Nkem ta rubuto ne daga Abuja