Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana cewa al’ummar Jihar Kano sun gamsu da takun gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa la’akari da irin muhimman ayyuka da ya gudanar cikin shekara ɗaya da kama mulki shi ya sa suke mara masa baya.
Babban mai taimakawa Gwamnan Jihar Kano akan harkar tsaftar muhalli, Hon. Ɗahiru Arrow Dakata ne ya bayyana haka da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin taron bikin Sallah da aka gudanar ba harabar gidan jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya ce duk mutumin da yake a cikin tsarin tafiyar Kwankwasiyya musamman gwamnati al’ummar Jihar Kano za su cigaba da mara masa baya da mararin sa da son sa, saboda ayyuka na alkhairi da akeyi musu.
Hon. Ɗahiru Arrow Dakatar ya ce suna sa rai da fatan nan da Shekaru uku masu zuwa makomar Jihar Kano a ƙarƙashin mulkin Abba Kabir Yusuf a tafiyar Kwankwasiyya al’ummar Jihar Kano musamman masu tasowa ta ɓ angaren harkar Ilimi sai Kano ta fita zakka a faɗin tarayyar ƙasar nan wajen bunƙasar Ilimi da ci gaban rayuwa.
Hon. Ɗahiru Arrow Dakata ya ce a matsayinsa na ɗan Kwankwasiyya abinda tsarin yake burge shi shine na yadda ake kula da na ƙasa da tallafawa talaka da mabuƙata wannan ne abinda ya sa suke tare da tsarin za su ci gaba da tafiya a kai da yardar Allah.
