Muna fuskantar matasalar ƙarancin kayan marmari a Gombe – Dauda Wanke

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

‘Yan kasuwar kayan marmari sun koka da ƙarancin kayan a wannan lokaci wanda rashin kayan ya sa sun koma kamar ‘yan zaman banza domin ƙarancin  kayan ya sa sun shiga ruɗu.

Dauda Malam Wanke wani mai sana’ar kayan marmari da ke sayar da kayan akan babbar hanyar zuwa gidan gwamnati a fadar jihar, ya koka matuƙa inda ya ce kayan ya yanke kuma ya yi tsada wanda suna ji suna gani sun zama Allah Sarki.

Ya ce abinda ya jawo rashin kayan shi ne lokacin sa ya yanke kuma wani bai fito ba kuma dama ana samun kayan ne daga jihar Benue musamman lemu da ayaba da abarba, amma kankana da sweet melon anan Gombe da jihar Bauchi aka neman su amma su din ma tsadar takin zamani ta shafe su inji shi.

A cewarsa jama’a suna buƙatar kayan duk da cewa kayan marmari ne amma ya yanke koda mutum yana da jarin sa da zai sayo kayan sai ya bi a hankali saboda kaɗan din da ake da shi ya yi matuƙar tsada kuma idan ka yi wasa sai su lalace kafin ya kare.

Har ila yau ya ce kaɗan ɗin da suke samu suna don ririta sana’ar shi din ma kafin su sayar wani lokacin suna tafka asara domin kafin ya kare wasu suna ruɓ ewa.

Dauda, ya ce ba yadda suka iya wannan sana’ar ita ce sana’ar da suke ci suke sha amma tana son ta gagare su domin sai anci an koshi sannan ake shan kayan marmari, amma da kafin rayuwar tayi tsada basu da matsala amma yanzu fa sai an tura su.

Duk da ma dai sana’ar akwai rufin asiri a cikin ta amma a halin yanzu fa sun shiga garari domin duk mai sana’a irin tasu idan aka ci gaba da tafiya a haka sai dai ya canja sana’a.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta dube su wajen samar musu da tallafi domin inganta sana;ar ko kuma su canja wata saboda kwari ce kuma ta zama kwarin su kuma suna da iyalai basu san wani hali za su kara shiga ba nan gaba saboda kayan ya yanke kuma ba su da wata sana’a sai ita.

By ukarofi