Tsaro: Majalisar Dattawa ta nemi a dakatar da siyasa a Kano da jihohi bakwai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta yi la’akari da ɗaukar matakan gaggawa, ciki har da yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a wasu jihohi takwas da ke sahun gaba wajen fama da matsalar tsaro, sakamakon yadda hare-haren ’yan ta’adda ke ƙara ƙamari a wasu sassan ƙasar.

Rahotanni sun nuna cewa wannan kira ya biyo bayan wani batu na gaggawa da Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya gabatar a zaman majalisar, inda ya jaddada cewa matsalar tsaro ba ta yankin guda ba ce, illa matsala ce ta ƙasa baki ɗaya da ke buƙatar kulawa ta musamman.

Sanatan ya gargaɗi takwarorinsa da kada su ɗauki lamarin da wasa, yana mai cewa zama a Abuja ba ya nufin matsalar tsaro ba ta shafe su ba. Ya kuma ba da shawarar a ɗauki matakin dakatar da duk wani aikin siyasa a faɗin ƙasa, ko aƙalla a jihohin da suka fi fuskantar barazanar tsaro kamar Borno, Filato, Bauchi, Benue, Neja, Sakkwato, Kebbi da wasu sassan Kano.

A cewarsa, irin wannan mataki zai ba da damar mayar da hankali gaba ɗaya wajen shawo kan matsalar tsaro kafin a koma harkokin siyasa. Ya ƙara da cewa ci gaba da yin ƙorafi ba tare da ɗaukar matakin da ya dace ba ba zai kawo sauyi ba.

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren ƙungiyar Boko Haram suka sake ƙaruwa a yankin Arewa maso Gabas, inda aka samu farmaki kan sansanonin soji da kuma sabbin barazanar hana ceto mutanen da aka sace.

A wani ɓangare na ƙudurin, Majalisar ta kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakin ceto mata, yara da tsofaffi sama da 400 da ake zargin suna hannun ’yan ta’adda a Jihar Borno tun ƙarshen watan Maris na shekarar 2026.

Sanata Tahir Monguno, wanda ya jagoranci gabatar da ƙudurin, ya bayyana damuwa matuƙa kan yadda hare-haren da ake kai wa sansanonin soji ke lalata nasarorin da aka samu a baya wajen yaƙi da ’yan tada kayar baya.

Shi ma Sanata Ali Ndume ya nuna damuwa kan halin da waɗanda aka sace ke ciki, yana mai cewa ’yan ta’addan sun yi barazanar watse su idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba. Haka zalika, Sanata Diket Plang ya bayyana cewa kai hare-hare kan jami’an tsaro na kara jefa tsoro a zukatan al’umma tare da nuna irin halin da tsaron ƙasa ke ciki.

Majalisar ta yi Allah-wadai da ci gaba da hare-haren Boko Haram kan rundunonin soji, tare da yin shiru na minti guda domin girmama sojojin da suka rasa rayukansu a fagen fama.

Har ila yau, ’yan majalisar sun buƙaci manyan hafsoshin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan yadda ake gudanar da ayyuka da kayan aiki a wuraren da hare-haren suka fi ƙamari, domin gano giɓi da gyara su.

Sun kuma buƙaci rundunar sojin ƙasa da ta ƙara bin dokokin yaƙi da na kare fararen hula, tare da bincikar duk wani zargi na cutar da jama’a yayin ayyukan soji.

Majalisar ta kuma yi kira ga al’ummomi da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci, tare da yabawa rundunar Operation Haɗin Kai bisa jajircewarta duk da ƙalubalen da take fuskanta.

Rahotanni na baya-bayan nan sun kuma nuna wani bidiyo da ake zargin wani ɓangare na Boko Haram ya fitar, inda aka ga wasu daga cikin mutanen da aka sace a yankin Ngoshe na ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, tare da barazanar daukar mataki mai tsauri idan ba a biya buƙatunsu cikin lokaci ba.

By ukarofi