Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayyana cikakkun dalilan da suka sa ta ƙi amincewa da buƙatar beli da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya gabatar, bayan fitar da sahihin kwafin hukuncinta (CTC) da aka yanke a ranar 21 ga Afrilu.
Alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Darius Khobo, ya ce barin El-Rufai a tsare yana da muhimmanci domin tabbatar da samuwarsa a kotu yayin da za a fara shari’a, yana mai jaddada cewa hakan ya dace da muradun adalci.
Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) ce ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin ba da kwangila ta hanyar yaudara da kuma karkatar da kuɗaɗen lamuni. Sai dai tsohon gwamnan ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.
An gudanar da zaman kotun ne a kulle, inda aka hana ’yan jarida shiga, sai dai daga bisani aka samu bayanai ta hanyar sahihin kwafin hukuncin da aka fitar.
A cikin bayanan kotun, an nuna cewa buƙatar belin ta dogara ne da hujjoji 24 da Muhammed Bala Aliyu ya gabatar, inda aka jaddada cewa laifukan ba na kisa ba ne, tare da bayyana matsayin El-Rufai a matsayin tsohon gwamna mai ƙarfi a cikin al’umma.
Haka kuma, an bayyana wa kotu cewa El-Rufai ya dawo daga ƙasar Masar da kansa, yana mai cewa zarge-zargen ba su da inganci, sannan ya nuna cewa yana fama da wasu matsalolin lafiya da ke buƙatar kulawa ta musamman.
Sai dai ICPC ta ƙi amincewa da buƙatar belin, inda ta gabatar da hujjoji guda tara ta bakin Idris Abubakar, tana mai cewa laifukan da ake zargin suna da nasaba da taɓarɓarewar tattalin arziki, tare da nuna damuwa kan yiwuwar katsalandan ga shaidu da kuma binciken da ke gudana kan wasu da ake zargi.
Hukumar ta kuma zargi El-Rufai da hana jami’an tsaro aikinsu a filin jirgin sama na Abuja a watan Fabrairu, tare da bayyana shi a matsayin wanda zai iya tserewa shari’a saboda matsayinsa a cikin al’umma.
Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya dage cewa buƙatar belin ta ginu ne kan tanade-tanaden kundin tsarin mulki da ke bai wa kowane mutum ’yancin walwala. Amma a gefe guda, lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya roƙi kotu da ta yi watsi da buƙatar, yana mai jaddada girman laifukan da ake zargi da kuma haɗarin katsalandan.
A hukuncinsa, Mai Shari’a Khobo ya bayyana cewa dogaro da matsayin El-Rufai a matsayin tsohon gwamna da minista “takobi ne mai kaifi biyu,” wato zai iya amfani ko cutar da shi.
Kotun ta kuma lura cewa El-Rufai bai gabatar da ƙarin hujjoji don karyata zarge-zargen ICPC ba, abin da ya sa aka ɗauki zarge-zargen a matsayin abin da bai fuskanci ƙalubale ba.
Game da batun lafiya, kotun ta ce babu wata hujja mai inganci da aka gabatar da za ta tabbatar da cewa yana da wata matsala da ke buƙatar a ba shi beli.
A ƙarshe, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar belin tare da umartar a ci gaba da tsare El-Rufai a hannun ICPC har sai an fara shari’a.
Haka kuma, kotun ta umarci a hanzarta gudanar da shari’ar, inda ɓangarorin biyu suka amince cewa za a fara sauraron shari’ar a makon farko na watan Yuni 2026.
An ɗage sauraron cikakkiyar ƙarar zuwa ranakun 1, 2, 3 da 4 ga Yuni, 2026.
