Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata gagarumar cakwakiya ta siyasa na kunno kai a Jihar Jigawa bayan Majalisar Dokokin Jihar ta ƙaddamar da wani bincike mai zurfi kan tsohon gwamnan jihar, Mohammed Badaru Abubakar, tare da shugabannin ƙananan hukumomi 27, bisa zargin almundahana da rashin sarrafa kuɗaɗen jama’a yadda ya kamata.
A zaman majalisar da aka gudanar, ’yan majalisar sun amince baki ɗaya da rahoton Kwamitin Asusun Jama’a, inda suka bayar da umarnin dawo da duk wasu kuɗaɗen da ake zargin an karkatar da su tsakanin shekarun 2019 zuwa 2024.
Shugaban kwamitin, Hon. Isyaku Abubakar, ya bayyana cewa binciken ya biyo bayan zaman sauraron ra’ayin jama’a da kuma nazarin rahotannin binciken kuɗi daga ofisoshin Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na jiha da na ƙananan hukumomi. Ya ce an tantance takardu da dama da suka haɗa da bayanan biyan kuɗi da kuma na saye-saye a ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati, ciki har da dukkan ƙananan hukumomi 27.
A yayin binciken, manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da kwamishinoni, manyan sakatarori da daraktocin kuɗi sun gurfana domin kare yadda suka tafiyar da dukiyar jama’a. Haka kuma shugabannin ƙananan hukumomi da wasu manyan jami’ansu sun fuskanci tsauraran tambayoyi kan yadda suka sarrafa kuɗaɗen da aka ba su.
Rahoton ya bankaɗo matsaloli masu tayar da hankali, inda a matakin jiha aka gano wuce gona da iri a kasafin kuɗi, rashin bin ƙa’idojin saye da sayarwa, da kuma gazawa wajen tattara kuɗaɗen shiga yadda ya kamata. A matakin aananan hukumomi kuwa, an gano ɓacewar takardu, biyan kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, da kuma kashe kuɗaɗe ba tare da hujja ba.
A wasu lokuta, an bayyana cewa an biya kuɗaɗe fiye da kima, wasu cak ba a iya tantance su ba, yayin da wasu muhimman takardu suka ɓace ko kuma aka lalata su da gangan.
Kwamitin ya jaddada cewa irin waɗannan kura-kurai suna lalata tsarin tafiyar da kuɗaɗe da kuma rage amincewar jama’a ga gwamnati. Saboda haka, ya bayar da shawarar a kwato duk kuɗaɗen da aka karkatar tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Baya ga haka, rahoton ya nuna akwai manyan matsaloli a tsarin aiki, ciki har da rashin ƙwararrun ma’aikatan kuɗi, raunin bin dokoki da kuma amfani da tsofaffin hanyoyin lissafi da ke sauƙaƙa maguɗi. Don haka majalisar na shirin kawo sauye-sauye, ciki har da tilasta wa jami’an kuɗi samun takardun ƙwarewa da kuma ƙarfafa ’yancin kan ofishin mai binciken kuɗaɗe.
Shugaban Majalisar, Hon. Haruna Aliyu, ya yaba wa kwamitin kan aikinsa, yana mai cewa za a miƙa rahoton ga ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakin gaggawa.
Sai dai kuma lokaci da yanayin ƙaddamar da binciken ya jawo muhawara a fagen siyasa, musamman ganin yadda aka kafa kwamitin sulhu kwanaki kaɗan kafin hakan domin sasanta rikicin siyasa tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan da na gwamna mai ci, Umar Namadi.
Masu sharhi na ganin binciken na iya wuce batun tantance kuɗaɗe kawai, domin yana iya girgiza tsarin siyasar jihar, musamman duba da cewa wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati na yanzu sun taɓa aiki a lokacin mulkin Badaru.
Yayin da sauye-sauyen siyasa ke ƙara ƙarfi, wannan bincike na iya zama abin da zai sauya makomar siyasar Jigawa gaba ɗaya.
