Tsofaffin ɗaliban Gumel Advanced Teachers College sun sake haɗuwa bayan shekara 40

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Kungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar Gumel Advanced Teachers College ta gudanar da taron haɗuwar tsofaffin ɗaliban da suka kammala karatu a makarantar shekaru 40 da suka gabata.

Shugaban ƙungiyar reshen Jihar Kano, Dakta Dahiru Abbas Kachako, ya ce an shirya taron ne domin ƙarfafa zumunci a tsakanin tsofaffin ɗaliban, tare da tallafa wa iyalan abokan karatunsu da suka rasu.

Ya bayyana cewa tun bayan kammala karatunsu, da yawa daga cikinsu ba su sake haɗuwa ba, yayin da wasu kuma suka riga mu gidan gaskiya.

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, Farfesa Yahaya Isa Bunkure, ya bayyana farin cikinsa bisa sake haɗuwa da abokan karatunsa da kuma malaman da suka koyar da su a lokacin da suke ɗalibai.

Ya ce irin wannan taro yana da matuƙar muhimmanci, domin yana ba tsofaffin ɗalibai damar sake haɗuwa da abokan karatunsu bayan shekaru masu yawa.

Bunkure ya kuma jaddada muhimmancin kafa ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai bayan kammala karatu, yana mai cewa hakan na ƙara dankon zumunci a tsakaninsu.

Haka kuma, wasu mambobin ƙungiyar da suka zanta da manema labarai, Alhaji Ibrahim Adamu Shamakeri da Hajiya Balaraba Adamu, sun bayyana cewa manufar shirya taron ita ce sake ganin juna da kuma murnar haɗuwar bayan dogon lokaci.

A yayin taron, an bayar da kyaututtuka ga waɗanda ke tallafa wa ƙungiyar, tare da iyalan wasu tsofaffin ɗaliban da suka rasu.

Da yake jawabi a madadin waɗanda aka karrama, Dakta Surajo Muhammad, wanda ya wakilci Sarkin Gumel, Alhaji Lawan Ahmed Muhammad, ya bayyana farin cikinsa bisa karramawar da aka yi wa sarkin.

Ya ce ƙungiyar ta yi abin da ya dace, bisa la’akari da cewa sarkin cikakken jagora ne kuma uba ga ƙungiyar, wanda a ko da yaushe ƙofarsa a buɗe take domin ganin ƙungiyar ta ci gaba, da kuma al’ummar masarautar Gumel.

An gudanar da taron ne a ɗakin taro na Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso, a Jihar Kano.

By ukarofi

Leave a Reply