Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Allah ya yi wa tsohon Allƙalin Kotun Ƙolin Nijeriya, Mai Shari’a Usman Muhammed Argungu rasuwa a safiyar yau Lahadi.
Marigayi Mai Shari’a Argungu ya rasu ne a gidansa dake garin Argungu a Jihar Kebbi bayan fama da wata jinya.
Ya rasu yana da shekaru 90 inda ya bar mata
ɗaya da ƴaƴa 12 waɗanda daga cikin su akwai alƙalan manyan kotuna da suka haɗa da; Alƙali Hassan Usman Muhammed da Alƙali Raliya Usman Muhammed da kuma jikoki sama da talatin.
Kafin rasuwarsa, ya yi aiki a matsayin Allƙalin Alƙalan ƙasar Gambia, babban Joji a jihohin Sokoto, Kano da Neja da kuma matsayin Alkali a kotun ɗaukaka ƙara a jihohin Legas da Kaduna inda daga ƙarshe ya zama Babban Alƙali a Kotun Ƙolin Nijeriya.
Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya bayyana rasuwar Alƙalin a matsayin babban rashi ba ga jihar Kebbi ko arewacin Nijeriya har ma ga ƙasa baki ɗaya saboda marigayin uba ne kuma shugaba ne abin koyi.
Ya yi addu’ar Allah ya jiƙansa ya bai wa iyalai da ƴan uwa haƙuri.
Tuni aka gudanar da jana’izarsa inda aka samu halartar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu; tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Babban Jojin Jihar Kebbi, tsohon Mataimakin Babban Kwanturola na kwastom Alhaji Ibrahim Muhammad Mera; Sakataren tsare-tsaren na Jam’iyyar APC na ƙasa, Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu; Ɗan majalisar dokokin jihar Kebbi, Honarabul Umar Na-amore; jami’an gwamnatin jihar Kebbi da Tarayya da dai sauransu.

