Hukumar ƴan sanda yankin Anambra ta bayyana cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon turmutsutsun jama’a a jihar ya kai 22, a cewar rahoton da aka bayar a ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce an fara bincike kan lamarin.
Ikenga, wanda shi ne babban sufeton ‘yan sanda, ya ce waɗanda suka ji raunuka suna karɓar magani a asibiti.
“Kwamishinan ‘yan sanda, Nnaghe Obono Itam, ya ziyarci asibitin da ake kula da waɗanda lamarin ya shafa, wanda ya faru a ranar 21/12/2024 a Okija, ƙaramar hukumar Ihiala, kuma ya bayyana cewa mutane 22 sun rasa rayukansu,” in ji Ikenga.
“Kwamishinan ya jajanta wa iyalai da abokan waɗanda suka rasu tare da yi wa waɗanda suka ji rauni fatan samun sauƙi cikin gaggawa.”
Turmutsutsun jama’ar ta faru ne a ranar Asabar yayin wani rabon shinkafa a filin wasa na Amaranta da ke Okija, Ihiala. Gidauniyar Obijackson ce ta shirya taron.
