Daga USMAN KAROFI
Hon. Abbas, wanda ya riƙe muƙamin kwamishinan raya karkara da cigaban al’umma har zuwa watan da ya gabata, ya bayyana ficewarsa daga NNPP ne yayin ziyarar da ya kai gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, a daren Juma’a.
Wannan sauyin sheƙa na Hon. Abbas ya kasance ci gaba da “Barau Tsunami” da ake kira, wanda ya jawo ɗaruruwan shugabannin NNPP tare da dubban magoya bayansu sun sauya sheƙa zuwa APC.
A cikin jawabinsa, Hon. Abbas ya bayyana cikakken goyon bayansa ga jam’iyyar APC tare da alƙawarin yin aiki don samun nasarar jam’iyyar a jihar Kano da ma ƙasar baki ɗaya. Sanata Barau Jibrin, wanda shi ne mataimakin kakakin majalisar ECOWAS, ya karɓi Hon. Abbas tare da Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas da wasu manyan shugabannin jam’iyyar. Sanatan ya bayyana farin cikin karɓar Hon. Abbas, wanda ya ce shi fitaccen ɗan siyasa ne mai kishin al’umma.
Sanata Barau ya tabbatar wa sabon ɗan jam’iyyar cewa APC za ta ba da cikakken goyon baya wajen ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya. Ya ƙara da cewa jam’iyyar tana da isasshen ƙarfin ɗaukar duk waɗanda ke son ci gaban ƙasa, tare da jaddada muhimmancin shugabanci nagari da aiki tuƙuru wajen inganta rayuwar al’umma.
Wannan ci gaba ya zo ne bayan NNPP ta rasa wasu jiga-jigan gwamnatinta, ciki har da sakataren gwamnatin jihar da wasu kwamishinoni guda biyar da aka sauke daga muƙamansu a watan da ya gabata.