Tsohon Ministan Noma, Abba Sayyadi Ruma, ya rasu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Allah ya yi wa tsohon Ministan Noma da Raya Karkara a zamanin Gwamnatin Marigayi Umaru Musa Yar’adua, Abba Sayyadi Ruma rasuwa.

Wata majiya ta bayyana cewa, tsohon ministan ya rasu ne a wani asibitin Landan da yammacin Laraba, yana da shekaru 69.

An haife shi a ranar 13 ga Maris, 1962, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin gudanarwa na Asusun Raya Aikin Noma na Duniya mai hedikwata a Rome na ƙasar Italiya.

Marigayin ya samu digirin farko a fannin tarihi a jami’ar Sokoto, da digiri na biyu a fannin harkokin ƙasa da ƙasa da diflomasiyya a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan ya samu digiri na uku a fannin hulɗa da ƙasa da ƙasa a jami’ar Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *