Uwar mulkin mallaka ta yi sabuwar firaminista

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Uwar ’yan mulkin mallaka ta duniya wato ƙasar Birtaniya ta yi sabuwar firaminista, Liz Truss bayan turka-turkar da ta kai ga kawar da firaministan ƙasar Boris Johnson. Tuni sarauniya Elizabeth ta tabbatar da wannan sabon juyi da ya kawo babbar jami’ar gwamnatin Johnson a matsayin jagorar ƙasar ta fuskar siyasa.

Yadda a kan samu sauyin jagoranci a Birtaniya na da ban sha’awa don in ka duba nau’in laifukan da kan kai ga ƙin jinin firaminista ba za su zama wani abun damuwa a wasu ƙasashe masu tutiyar dimkoraɗiyya ba.

Rashin da’a da taurin kai ko halin ko in kula na daga dalilan da su ka cinye Johnson. Wani dalili ma mai ban dariya shi ne jagorantar wani taro mai taƙaitattun mutane a lokacin da duniya ta ke cikin firgicin cutar annoba.

Tun lokacin da Johnson ya jagoranci taron a ke ta magana a kai cewa ya taka doka don neman yaɗa cutar a ƙasar da ta yi matuƙar firgita da cutar. Ka ga wannan na nuna ba a son mai dokar barci ya buge da gyangyaɗi a ƙasar Birtaniya.

In mun kwatanta hakan da wasu ƙasashen za mu ga manyan jami’an gwamnati sun fi ƙarfin doka ko kuma a ce su ne ma dokar don haka za su yi abin da su ka ga dama amma baa bun da zai same su sai ma ka ga jami’an tsaro da manyan bindigogi na raka su ko ina za su don kare lafiyarsu da lafiyar iyalin su da sauran ’yan uwan su ko ma ya haɗa har da ’yan amshin shatarsu.

Na taɓa ganin wani faifan bidiyo da ya nuna Johnson ya shiga wani shago ya sayi kayan da ya ke buƙata inda ya fito ya ɗauki keken sa yi yi gaba shi kaɗai ba tare da wani hadimi da aƙalla zai riƙe ma sa kayan ba.

A ina wasu ƙasashe irin na Afirka ko da an samu zaman lafiya za su ga shugabannin na yawo ba tare da ’yan ba ni na iya ba. Ba ta yadda za a yi wani shugaba ya fito ba mota 20 ta ’yan za ni ne ta tadda mu je da za ka ga su na tare da shi.

Ba ma kawai za a kare a yawan motocin ba ne, a’a can kafin a tsaya ma za ka ga wasu da baƙaƙen kaya sun bazamo a guje kamar ran su zai fita su na raka motar shugaba da sam-sam harsashi ba ya huda ta amma su zai iya huda su!

Cikin dalilan da a ka zargi Johnson da ya kai ga rasa muqaminsa na jam’iyyar ’yan mazan jiya wato KONZABATIB akwai taurin kai wanda hakan kuma tun ya na makaranta ya ke da wannan ɗabi’ar. Hakanan tsarin masha’a ba ya tayar ma sa hankali ko ma a ce ya kan ma burge shi ne.

Duk yadda a ke ta sukar Johnson bai sa ya gyara ɗabi’arsa ba ta daurewa ’yan duniya hayaqin taba baya. Duk da ɗabi’ar ta sa mummuna ce amma wannan ya nuna a Birtaniya ba munafurci irin yadda wasu jagorori ke yi na Annabi Musa a fuska Fir’auna a zuci.

Yadda a ka yi ta rorewa a na ficewa daga gwamnatin Johnson bai sa ya girgiza ba. In za a tuna dalilin rashin goyon baya ko cimmawa ’yan Birtaniya burin ficewa daga ƙungiyar tarayyar Turai ya sa tsohon firaminista David Cameron ya rasa muƙamin sa. Duk da yanda Johnson ya biyewa ra’ayin ’yan ƙasar bai hana su juya ma sa baya ba musamman daga jam’iyyar sa ta KONZATIB.

Abin da ya fito fili a tsarin Turawa shi ne duk abun da mutum ya ke sha’awar yi ya fito fili ya yi abun sa in ya so ko doka ta yi aiki a kan sa amma ba za a ce ya ji kunya ba. In za a tuna ko akasin da ya faru da tsohon shugaban Amurka Bill Clintron na Monica Lewinsky bai zama laifi ba sai dai tuhumar yin ƙarya ko ɓoye gaskiyar lamarin da Clinton ya yi daga farko kafin bincike ya tabbatar.

Ma’ana inda Clinton ya nuna ya aikata laifin kuma ya na neman afuwar jama’a shikenan maganar sai ta mutu murus. Gaskiya abun da ya kwantar da maganar zargin lalatar Clinton shi ne yafiyar da matar sa Hillary ta yi wa mijin ta. Idan ba ta yafe ba da gaskiya zai samu gagarumar matsala.

Kuma wani tsarin shi ne maimakon ta musanta bayanin da zargin a na neman ƙalawa mijin ta sharri ne, ba ta yi hakan ba, kuma ta karɓi laifin da mijin ta ya yi da hannu biyu da tausaya ma sa ta hanyar yafe ma sa. Wannan mataki ya sa farin jinin Clinton bai gama dushewa ba don in an tuna tsohon mataimakinsa Albert Arnold Gore da ya samu takarar shugabancin ƙasar bai yarda Clinton ya raka shi kamfen ba don gudun kar ya shafa ma sa kashin kajin Lewinsky.

Duk da da hakan dabarar ba ta yi tasiri ba don ɗan takarar Rifabulikan George W. Bush ya yi nasara a kan sa ya kawar da ’yan Dimokrats daga fadar WHITE HOUSE. Har gobe Clinton na da magoya baya a Amurka da kuma ’yan takarar jam’iyyarsa za su so ya mara mu su baya kamar yadda tsohon shugaban ƙasar Barack Obama ya ke da wannan tasiri.

A duk ƙasar da dimokraɗiyyar ta ta yi ƙarfi za ka samu ƙorafin mutane ya na da tasiri. Duk inda ba lalle tsarin zaɓen adalci ko manufofi na gaskiya da adalci kan kawo jagorori kan mulki ba, za ka samu kukan mutane tamkar dariya su ke yi don ko kusa ba mai share mu su hawaye.

Ya kamata duk gwamnatin da a ke yi wa ta ke da ta jama’a ce kuma daga jama’a zuwa ga jama’a ta riƙa mutunta muradu da ra’ayoyin jama’ar. Idan dimokuraɗiyya ba za ta iya sauraron jama’a ba sai ma harara, ɗauri da jefa borkonon tsohuwa, gaskiya wannan ba dimokuraɗiyya ba ce murƙushaɗiyya ce.

Masana kimiyyar siyasa na bayyana cewa ƙalubalen tattalin arziki da matsalolin da ta gada daga gwamnatin Boris Johnson, zai zama daga manyan ƙalubale gaban sabuwar firaministar Burtaniya Liz Truss.

Liz Truss wacce tsohuwar sakatariyar wajen Birtaniya ce ta zama sabuwar firaministar ƙasar bayan zaven ta a matsayin shugabar jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya KONZABATIB.

Truss dai ta gaji muƙami daga tsohon firaminista Boris Johnson wanda ya fuskanci juya baya hatta daga jami’an gwamnatinsa in ka deɓe irin Truss ɗin da ta bi a hankali har faɗuwar gwamnatin. Wato duk wainar da a ka toya a gwamnatin Johnson da Truss a ka yi kuma ba ta watsar da Johnson din ba har ƙarshen gwamnatin.

Truss ta riƙe muƙamai da dama har ta kai ga an sanya ta a jerin ’yan sahun farko a jam’iyyar KONZABATIB. Samun muƙamin na ta ba lalle ya zama wani babban abun mamaki ba don kazalika ba ma ita ce mace ta farko da ta zama firaministar Birtaniya ba.

Masanin kimiyyar siyasa na tsangayar siyasa a jami’ar Abuja Dr.Farouk BB Farouk ya ce Truss za ta iya fuskantar turjiya daga masu matuƙar hamayya da manufofin ko-in-kula na Johnson da kuma ba ta yi adawa da hakan ba.

Kazalika Dr.Farouk ya nuna matsalar tattalin arziki da ta sa lalle mutane na buƙatar tallafi ka iya zama wata babbar damuwa don Truss ta qi amincewa da qarin haraji don daidaita tattalin arzikin kamar yadda wanda ta kayar a zaɓen Rishi Sunak ke fatar aiwatarwa. Kuma a gaskiya akwai taɓaɓar ko Birtaniya na da karfin arzikin yi wa ’yan ƙasar tallafi.

A nan Dr.Farouk ya ce sai Truss ta jajirce kafin madafun iko su zauna ram a hannun ta ‘akwai gungun masu adawa da tsarin Boris Johnson wanda zai iya cigaba da tasiri a cikin mulkin ta’. Kuma za a samu wasu jami’an da za su cigaba da jingine mukaminsu a gwamnatin ta gida mai lamba 10 a titin Downing da ke birnin Landan.

Liz Truss da a ka haifa a shekarar 1975 ta zama mace ta uku da ta zama firaministar Birtaniya bayan Margaret Thatcher da Theresa May.

Kammalawa;

Ya zama mai muhimmanci a duk tsarin dimokraɗiyya a rika samun sauyi in waɗanda ke madafun iko sun saɓa alƙawari ko sun taka dokokin ƙasar da su ke mulka. Su kan su jagororin ya dace a ga sun yi murabus matuƙar sun ga ɗabi’ar su ba za ta mutunta wata dokar ƙasa ba.

Misali a ce shan taba haramun ne a cikin ofishin gwamnati, to in har wani mashayin taba ya ga lalle shi ya kan sha taba a ofis kafin samun muqami kuma ba zai iya dainawa ba sai ya ƙi yarda a rantsar da shi don cigaba da shan tabarsa a can ofishin san a ƙashin kai.

Yanzu dokoki na wa shugabannin ƙasashen da su ka yi aron mulkin dimokuraɗiyya su ke takawa amma su na nan daram a kan mulki kuma har son samu ma su maƙale a madafun iko har na rai da rai?

By Editor