Uwargidan Gwamnan Zamfara ta yi jimamin rasuwar Sarkin Gusau

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bayyana kaɗuwar ta bisa rasuwar Mai Martaba Sarkin Gusau, Alhaji (Dr.) Ibrahim Bello, Sarkin Gusau wanda ya rasu a wani asibiti da ke Abuja ranar Alhamis.

Babbar mataimakiya ta musamman kan harkokin yaɗa labarai a ofishin Uwargidan Gwamnan, Rabi’atu Yusuf ta fitar da sanarwar.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana rasuwar mai martaba sarkin a matsayin ba kawai rashi ga iyalansa ba har ma da babban rashi ga masarautar Gusau da al’ummar Jihar Zamfara da Najeriya baki ɗaya.

A cewarta, marigayi sarki uba ne kuma fitaccen sarkin gargajiya wanda mulkinsa ke da mutunci da hikima da kuma sadaukar da kai ga zaman lafiya da ci gaba.

“Tun da ya hau kan karagar mulki, Dakta Ibrahim Bello ya duƙufa da dukan zuciyarsa wajen yi wa al’ummarsa hidima cikin tawali’u da tausayi da kuma zurfin fahimtar buƙatun su, inda shugabancinsa ya sa ya samu ƙauna da mutunta al’ummarsa da kuma girmama wasu da dama da ke bayan iyakokin Jihar Zamfara,” inji ta.

Uwargidan gwamnan ta bayyana cewa rasuwar sarkin ya haifar da ɗa mai ido a cibiyar gargajiya ta Gusau, wanda zai yi wuyar cikawa. Ta ƙara da cewa abin da ya gada na hidimar sadaukar da kai da kuma shugabanci nagari zai ci gaba da wanzuwa a cikin zukata da tunanin waɗanda ya jagoranta da banbanci.

Ta kuma yi ta’aziyya ga iyalan gidan sarauta, masarautar Gusau, da ɗaukacin al’ummar Jihar Zamfara bisa rasuwarsa.

Hakazalika tayi addu’ar Allah SWT ya gafarta masa kurakuran sa, ya kuma saka masa da kyawawan ayyukansa, ya kuma ba shi gidan aljannatul Firdausi.

By ukarofi