Wacce gudunmawa ka ke bayarwa wajen samar da zaman lafiya?

Spread the love

Mai karatu barkanmu da sake saduwa a wani karo na wannan fili na ra’ayi, wanda yake ba mu damar tura wasiƙunmu a jaridar Blueprint Manhaja mai albarka. Ina ƙara ankarar da mu, musamman matasanmu game da abubuwa ko hanyoyin da za a bi wajen cigaban al’umma a harkokin yau da kullum, wanda kuma wannan abu yana ƙunshe ne a hanyoyi da dama, ta yadda kowa da irin gudunmawar da zai bayar a cimma nasarar abin.

Ga duk mai bibiyar wannan shafi namu zai lura da cewa mun fi mayar da hakali ne wajen wasu muhimman abubuwa guda biyu, waɗanda suka haɗa da harkar ci gaban matasa da kuma harkar samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Tabbas ko ba a faɗa ba, waɗannan abubuwa guda biyu su ne ginshiƙan ci gaban kowace al’umma daga kowace nahiya, musamman bisa la’akari da cewa matasa ne suka fi yawa a cikin al’umma, kuma su ne ake amfani da su wajen samar da rashin zaman lafiya. Don haka za mu iya cewa abubuwan nan guda biyu tamkar abu ɗaya ne.

Saboda haka ko a yau ma maudu’in namu yana nan a wannan ɗabaƙa ne, domin yana da muhimmanci mutum ya kasance yana ankare da duk wani abin da zai kasance na tashin hankali ne, mutumin nan kuwa matashi ne ko dattijo. Za a iya gane haka ta hanyar mu’amalar mutum da jama’ar da yake cuɗanya da ita.

Ko da wane lokaci yana da muhimmanci mutum ya zama yana duba abubuwan da za su kawo ci gaban al’umma, musamman ta fannin samar da zaman lafiya da fahimtar juna, mutum ya ga cewa wace gudumawa yake bayarwa don samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummarsa da yake zaune a ciki.

Kada ke nan ya kasance ya zama wanda a kullum shi ba shi da wani aiki sai haddasa fitina, ko kuma neman haɗa wani da wani, ko kuma mutum ya ware kansa ya rinƙa yin abubuwa shi kaɗai, wato tamkar yana ƙyamar jama’ar da yake zaune a ciki.

A watannin baya na taɓa yin wani rubutu a wannan shafi game da batun nan na yadda wasu kan saki bakinsu wajen furta duk abin da ya fito, ba tare da tunanin matsalar da zai iya haifarwa ba, mutum ya saki ya jefa magana mai zafi, wacce ya san za ta ɓata wa abokin zaman sa rai.

Lallai ko shakka babu, kowane mutum da Allah ya yi, ya yi shi da irin nasa tunanin, kowa da yadda yake kallon abu idan ya zo masa, kamar yadda yake kuma kowa da irin nasa ra’ayin. Wasu ana iya kawar da su daga kan ra’ayinsu mummuna ko kyakkyawa, wasu kuma ba yadda za a yi a iya kawar da su daga ra’ayin da suka ginu a kai.

Irin wannan ra’ayi da fahimta da Allah ya yi wa kowa tasa daban, shi ne ya kamata a ce kowa ya tsaya a kan nasa, kada wani ya ce dole sai kowa ya bar nasa ya dawo nasa. Idan kowa ya riƙe nasa, to ba yadda za a a ce an samu wata hatsaniya game da fahimtar wani. Kamar yadda karin maganar Hausawa ke cewa ‘DUNIYA ZAMAN DAN MARINA, KOWA DA INDA YA SA GABANSA!’

A irin wannan yanayi ne ya zama sai ka taras da wani ko wasu suna furta kalaman da za su kawo ruɗani, wani lokaci ma har yakan kai ga jawo tashin hankali a tsakanin jama’a. Duk irin waɗannan abubuwa, ba wani abu ke jawo su ba illa rashin girmama addini, fahimta, ƙabila ko martabar wani, wanda hakan kuma ke zama babbar barazana ga zaman lafiyar al’umma. Domin wajibi ne, muddun ana tare, to a girmama juna.

Kalaman ɓatanci, ba abin da suke jawowa illa rarraba da tashin hankali a tsakanin jama’a. Wasu lokulata ma, abin takaici za ka taras da irin waɗannan kalaman suna fitowa ne daga bakin shugabannin addini, waɗanda suka haɗa da Malamai da Fastoci, wanda maimakon su zama masu haɗa kan al’umma, sai ya zama sun zama masu rabawa, ta yadda za ka ga wasu shugabannin addinin sun bar koyarwar addinin nasu sun koma suna bin ra’ayin kansu, kuma da haka suke jan magoya bayana.

Haka kuma ko ma a cikin addinin, mutum zai taras da cewa ya-su ya-su ma suna cusa irin wannan ƙiyayya ta hanyar furta kalaman ɓantanci da cusa ƙiyayya ga mabiyansu na sauran al’ummar da suke da bambancin fahimta ko ra’ayi da su, inda a wasu lokuta abin har ya kan kai ga zubar da jini. Abin baƙin cikin ma wasu lokuta za ka taras da ’yan gida ɗaya ne, amma ba a ga-maciji da juna.

Baya ga addini, wani ɓangare kuma da ake amfani da irin waɗannan kalamai na cusa ƙiyayya a tsakanin al’umma, shi ne ɓangaren siyasa, wanda za a iya cewa kamar abin ya fi muni ta nan. Domin za ka ga ɗan siyasa ya dage yana ta furta kalamai na ɓatanci, wanda zai cusa mummanar ƙiyayya idan abokin hamayyarsa ya ji, wanda ta haka sai ya a ginu a cikin ƙiyayya da gaba.

Baya ga fannonin addini da siyasa, hatta a tsakanin jama’a ma akwai lokutan da wasu jama’a za su rinƙa furta irin waɗannan kalamai na cusa ƙiyayya da ɓatanci, wasu lokuta kawai don su haddasa gaba da ƙiyayya, ko kuma don cimma wata manufa tasu ta ƙashin kansu. Ta yadda za ka ga wasu lokuta ko a cikin hira ma sai kawai ka ji mutum ya soka wa ɗan uwansa wata magana, wanda in ba hankali aka yi ba, nan da nan sai a tashi da tsiya.

Saboda haka yana da muhimmanci kowa ya san yadda zai rinƙa tafiyar da harkokinsa na zamantakewa a tsakanin jama’a, kowa ya san mene ne idan ya furta zai zama ya ɓata ma abokin zamansa rai, mene ne kuma zai yi wanda zai zama ya samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.

Wannan shi ne abin da ya wajaba kowa ya mayar da hankali a kai. Muna fata Allah ya shige mana gaba ya yi mana jagoranci a duk harkokinmu nay au da kullum.

Alkazeem M. Shareef Alhasan, 08062740226

By ukarofi